logo

HAUSA

Mayar da Afghanistan saniyar ware ba zai haifar da da mai ido ba ga duniya

2021-09-14 14:52:59 CRI

Mayar da Afghanistan saniyar ware ba zai haifar da da mai ido ba ga duniya_fororder_A

Yayin da kasashen duniya suka yi biris, har ma wasu hukumomi ke gargadi game da zuba kudade, Kasar Sin a matsayinta na makwabciya kuma babbar kasa, ta sanar da cewa zata gaggauta bayar da gudunmuwar alluran riga kafin COVID-19 da yawansa a matakin farko zai kai miliyan 3 da kayayyakin abinci da rigunan sanyi da magunguna ga kasar Afghanistan, wadanda darajarsu ta kai yuan biliyan 200.

Idan aka yi la’akari da yanayin da duniya ke ciki saboda annobar COVID-19 da sauran abubuwan dake faruwa tsakanin kasa da kasa da kuma cikin kasashe daban-daban, tunanin taimakawa wata kasa dake cikin mawuyacin hali, abu ne da ya yi matukar dacewa.

Hakika Sin ta yi kaifin tunani na gaggauta kai dauki ga al’ummar kasar. Aminiyar kwarai, ita ce ke tsaya komai wuya komai dadi. Kuma dama an ce baka sanin mai kaunarka, sai ka shiga cikin matsala. Bayan shafe shekaru 20 da mamaye kasar Afghanistan, babu abun da Amurka ta tabuka face jefa fararen hula cikin tasku, kuma cikin kankanin lokaci da janyewarta, sai ga kungiyar Taliban din ta yi ikirarin yaka, ta fito da karfinta ba tare da wani jinkiri ba, lamarin da ya shaida cewa, a duk wadannan shekaru da Amurka ta diba a Afghanistan, babu wani abun arziki da ta tabuka.

Mayar da Afghanistan saniyar ware ba zai haifar da da mai ido ba ga duniya_fororder_B

Muddun ana son ceton Afghanistan da sauran sassan duniya, taimakawa kasar farfadowa ya zama abun da ya wajaba. Rahotanni na cewa, mutum daya cikin 3, ba su da hanyar samun abinci a kasar. Kana talauci ya karu, baya ga mutane kusan miliyan uku da suka rasa matsugunansu, baya ga fari da kasar ke fama da shi.

Babban abun da kasashen duniya ya kamata su sa a gaba shi ne, watsi da burinsu na siyasa, su taimaka a gudu tare a tsira tare. Domin kamar yadda kasar Sin ke cewa, makoma ta bai daya dukkan bil adama ke da shi, don haka, muddun wata kasa tana cikin tashin hankali, to hakan na iya shafar sauran kasashe.  

Mayar da Afghanistan saniyar ware a duniya, zai kara durkusar da tattalin arzikin kasar kamar dai yadda tarihi ya nuna a baya, sai dai taimako daga babbar kasa kuma makwabciya kamar Sin, wadda ke girmama cikakken ‘yanci da manufofin kasashe ba tare da tsoma musu baki cikin harkokinsu na gida ba, zai taimaka gaya wajen farfado da kasar daga halin da take ciki, da kyautata rayuwar al’ummarta. (Fa'iza Mustapha)