Manufar samar da abinci ta kasar Sin ya zama darasi ga Afrika yayin fama da annoba
2021-09-13 17:15:46 CRI
Kokarin da kasar Sin ke yi wajen kiyaye manufofinta na samar da abinci da bunkasa aikin gona a yayin da ake fama da annobar COVID-19 ya kasance babban darasi ga kasashen Afrika, kamar yadda masana suka bayyana. Dama dai an ce, “Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.” Har kullum masu rike da madafun iko a kasar Sin suna cigaba da yin bakin kokarinsu wajen tabbatar da burin gwamnatin kasar na wadata al’ummun Sinawa da abinci duk da yawan al’ummar da kasar ke da shi wanda ya zarce biliyan 1.4. Manufofin gwamnatin kan wadata al’umma da abinci muhimmin batu ne wanda mahukunta ke dora muhimmanci kansa, koda a karshen makon da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wata wasika don taya murnar bude taron rage yawan hasarar hatsi na kasa da kasa. Inda ya yi nuni da cewa, batun wadatar hatsi muhimmin aiki ne dake da alaka da rayuwar bil Adama, rage yawan hasarar hatsi ya zama hanyar da ta dace don tabbatar da isashen hatsi. Ya ce a halin yanzu, COVID-19 na kan ganiyarta a duniya, ana fuskantar matsalar karancin hatsi, kamata ya yi kasashe daban-daban su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba don rage yawan hasarar.
Masana a Afrika suna ganin cewa, ya dace kasashen Afrika su koyi darasi daga kasar Sin game da matakan da take dauka wajen wadata al’ummarta da abinci, duk kuwa da yawan al’ummar da kasar ta Sin ke da shi. A cikin jawaban da masanan suka gabatar a wajen taron kolin bunkasa aikin gona na Afrika wato AGRF na 2021 da aka shirya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, sun bayyana cewa, ya kamata kasashen Afrika su rungumi ingantaccen tsarin da kasar Sin ke amfani da shi wanda ya kunshi amfani da tsarin ciniki ta intanet domin rage illolin da annobar ke haifarwa ga fannin ayyukan gona da hada hadar kasuwancinsu. Fadel Ndiame, mataimakin shugaban gamayyar kungiyar bunkasa ayyukan gona ta Afrika, AGRF, dake da ofishinta a Nairobi, ya ce, kamata ya yi fannin aikin gona ya zamo wani muhimmin jigo na hadin gwiwar Sin da Afrika. Ya kara da cewa, fannin yana da matukar alfanu wanda ya hada da farfado da tattalin arzikin mazauna karkara, samar da abinci, da samar da guraben ayyukan dogaro da kai ga matasa. Haka zalika, shugabannin hukumomin gwamnatocin kasashen yankin Hamadar Afrika sun jaddada aniyarsu game da ajandar samar da abinci a matsayin wani bangare na shirin farfadowa daga annobar COVID-19. Lokaci ya yi da ya kamata a sauya salon ayyukan noma a Afrika domin bunakasa samar da abinci, da tabbatar da inganta samar da sinadarai masu gina jiki da bunkasa hanyoyin samun kudaden shigar mazauna karkara yayin da nahiyar ke fadi-tashin neman farfadowa daga mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar. (Ahmad Fagam)