Sharhi:Danne hakkin dan Adam ne yadda ake siyasantar da aikin yakar ta’ddanci
2021-09-13 21:34:51 CRI
A yayin bikin tunawa da cika shekaru 10 da harin kunar bakin wake da aka kai wa ginin ofishin MDD da ke birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, David Ilya, mai shekaru 9 da haihuwa ya isa dandamalin tunawa da wadanda harin ya rutsa da su, don aza furen martaba wadanda suka rasu yayin harin.
A ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2011, wata mota cike da albarusai, ta kutse cikin harabar ofishin MDD da ke Nijeriya, wadda daga bisani ta tarwatse, harin da ya hallaka mutane 23, a yayin da sama da 60 suka ji raunuka. Musa Ilya, mahaifin David Ilya, wanda ya yi aiki da hukumar UNDP, yana daga cikin wadanda harin ya hallaka.
Da mai dakinsa Sarah ta ji labarin rasuwarsa, ta yi matukar bakin ciki har ta suma, kuma a lokacin Sarah tana da ciki, baya ga yara biyar da suke da shi. Bayan wata guda ne kuma, aka haifi David Ilya, wanda ya zama dan autan gidan.
Harin ya girgiza iyalan wadannan mutane 23 da ya hallaka, sai dai ba su ne kadai ke shan wahalar ta’addanci ba.
Kungiyar Boko Haram tun bayan kafuwarta a kusan shekaru 20 da suka wuce, ta sha kaddamar da hare-hare kan fararen hula, da sojoji, da ‘yan sanda a Nijeriya, da ma kasashe makwabtanta, hare-haren da suka haddasa hasarorin rayuka kimanin dubu 30, tare da raba mutane miliyan biyu da muhallinsu, wanda hakan ya haifar da babbar barazana ga yankunan yammacin Afirka.
Kamar yadda yake a Nijeriya, ta’addanci ma ya addabi kasar Sin. Tun daga shekarun 1990 zuwa shekarar 2016, rukunonin masu ra’ayin ta’addanci, da masu tsattsauran ra’ayi, da ma masu ra’ayin janyo baraka ga kasa na cikin gida da wajen kasar Sin, sun kaddamar da dubban hare-haren ta’addanci a jihar Xinjiang ta kasar, wadanda suka hallaka fararen hula masu dimbin yawa.
Domin yakar ta’addanci da ma kiyaye tsaron al’umma, gwamnatin kasar Sin ta karfafa matakan tsaro a jihar Xinjiang, tare da kafa wasu cibiyoyin horas da ilmin sana’o’i, a wani kokari na taimakawa matasa da suka sha tasirin tsattsauran ra’ayi, don su samu abin da za su iya dogaro a kai, ta yadda za a kawar da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi daga tushensu. Bisa namijin kokarin da aka yi a shekaru da suka wuce, yanayin tsaro ya inganta sosai a jihar, inda ba a samu faruwar harin ta’addanci ba ko guda daga shekarar 2016 zuwa yanzu.
Sai dai abin baki ciki shi ne, yadda Amurka da kawayenta suka yi biris da kwanciyar hankali da ma ci gaba da aka samu a jihar Xinjiang, kuma suka yi ta fakewa da sunan kare hakkin bil Adam wajen shafa wa kasar Sin kashin kaji bisa batun Xinjiang, don neman tsoma baki cikin harkokin gida na kasar, duk da cewa su kansu ma ta’addanci ke addabarsu.
Kwanan nan, kotun musamman ta Uygur da Amurka da wasu kasashen yamma, da ma kungiyar East Turkestan suka kafa, ta gudanar da zaman sauraro a karo na biyu. Lallai, a yayin da ake cika shekaru 20 da harin ta’addanci na “9.11” , yadda aka dauki wannan mataki ya wulakanta wadanda ‘yan ta’adda suka hallaka a jihar Xinjiang, haka kuma ya kasance kalubale ga al’ummar duniya da ke fuskantar barazanar ta’addanci, haka kuma keta hakkin bil Adam ne zalla. Kada a manta, a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, Amurkawa kusan 3000 ne suka rasa rayukansu, a yayin da tagwayen gine-ginen da aka kaiwa hari suka rushe, lallai wannan ba abin bakin ciki ga jama’ar Amurka kawai ba ne, hatta ma ga ‘yan Adam baki daya.
Duk da haka, Amurka da ma wasu kasashe sun yi ta nuna fuska biyu wajen yaki da ta’addanci, inda suke yin amfani da ‘yan ta’adda da a ganinta ba za su yi mata illa ba, a yayin da kuma take iya kokarinta wajen yakar ‘yan ta’adda da ke mata illa da barazana. Lallai yadda Amurka da mabiyanta suke siyasantar da aikin yaki da ta’addanci ya gurgunta aikin da kasa da kasa ke yi na yaki da ta’addanci.
A gun taron kolin tunawa da cikar MDD shekaru 75 da kafuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya yi nuni da cewa, tuni ‘yan Adam suka shiga zamani na cude-ni-in-cude-ka, don haka kasa da kasa na dogara ga juna, kuma makomarsu daya ce, don haka, ya kamata kasa da kasa su hada kansu wajen tinkarar barazana da kalubale na baki daya da ke gabansu.
Ta’addanci barazana ce da ‘yan Adam baki daya ke fuskanta. Kuma kamata ya yi a daina nuna fuska biyu tare da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, domin ta hakan ne za a kai ga kawo karshensa. (Lubabatu Lei)