logo

HAUSA

Lokaci Ya Yi Da Za A Binciki Kasar Amurka Kan Asalin Tayar Da Yaki

2021-09-13 21:59:51 cri

Lokaci Ya Yi Da Za A Binciki Kasar Amurka Kan Asalin Tayar Da Yaki_fororder_微信图片_20210913215912

A ranar 13 da 14 ga wata, sakataren harkokin wajen Amurka  Antony Blinken, zai halarci zaman sauraron ra’ayi na majalisar dokokin kasar kan batun janye sojoji daga Afghanistan. Kafin haka, kafofin watsa labarai na Amurka sun yi nuni da cewa, Blinken ba zai iya kare laifin janye sojojin Amurka daga Afghanistan ba, kuma ana tsammanin zai fuskanci tambayoyi masu tsanani yayin ba da shaida.

A hakika dai, wannan taron sauraren ra’ayoyi, zai kuma zama tamkar wata taga ga duniya, a fannin fahimtar asalin tayar da yaki na Amurka.

A matsayinta na wata kasa mai tarihi na shekaru sama da 240 kacal, Amurka ta tayar, da kuma shiga yake-yake sama da 200. Babu shakka Amurka ita ce kasa mafi sha’awar yaki a duniya. Domin nuna danniya ko babakere irin na Amurka, wasu 'yan siyasar kasar suna daukar matakin soji, don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe, da yada ra’ayin darajta Amurka, har ma da murkushe mulkin wasu kasashe.

A gefe guda, dalilin da ya sa kasar Amurka ke sha’awa sosai kan yaki, shi ne yin la’akari da moriyar tattalin arziki. Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya taba nuna cewa, Amurka na fatan a ci gaba da yake-yake, domin wasu kasashe za su sayi jiragen sama, da jiragen ruwa na yaki, da harsasai na Amurka. Kuma a duk lokacin da yakin ya kare, dimbin mutane a Amurka za su rasa ayyukan yi.

A sa'i daya kuma, kasar Amurka ta kuma yi kokarin sauya wasu kasashe bisa ga ra’ayinta, ta yi kokarin aiwatar da dimokuradiyya samfurin ta a wadannan kasashe, sakamakon ba tare da wani bambanci ba ta ci hasara, wanda ya haifar da mummunan bala'i ga jama'ar kasashen. (Mai fassara: Bilkisu)