logo

HAUSA

Habasha ta yi bikin sabuwar shekara ta kasar tare da fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali

2021-09-12 17:35:45 CRI

Habasha ta yi bikin sabuwar shekara ta kasar tare da fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali_fororder_1083982447769813005_ph

A ranar Asabar al’ummar kasar Habasha sun shiga ranar farko ta sabuwar shekarar kasar, yayin da kasar ta yi maraba da shekarar 2014 tare da fatan samun dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.

Kasar ta gabashin Afrika, tana amfani da kalantar musamman, inda kasar ke lissafin shekararta wacce ke da bambancin shekaru bakwai zuwa takwas a bisa lissafin kalantar meladiyya. A halin yanzu, kasar tana bikin zuwan sabuwar shekarar 2014 ne.

Yayin da al’ummar Habasha suka fuskanci mummunan tashin hankalin da ya haifar da hasarar rayuka a shekarar da ta gabata sakamakon rikicin da ya barke a yankin Tigray da ke arewacin kasar, inda aka gwabza yaki tsakanin dakarun gwamnati da mayakan ‘yan tawaye, wanda a yanzu rikicin ya watsu zuwa makwabtan yankunan Afar da Amhara, a yanzu al’ummar kasar Habasha suna murnar sabuwar shekarar a cikin yanayin damuwa.

Bayan burin da suke da shi na ganin karshen tashin hankali na baya bayan nan dake cigaba da ta’zzara, haka kuma, al’ummar kasar Habasha suna fatan fara sabuwar shekarar ta 2014 wajen samun daidaituwar al’amurran tattalin arzikin kasa wanda ya gamu da cikas sakamakon tasirin barkewar annobar COVID-19.

Firaministan kasar Habasha, Abiy Ahmed, wanda ke bikin sabuwar shekarar tare da dakarun tsaron kasar Habasha wadanda suke aiki a bakin daga, ya baiwa al’ummar kasar Habasha tabbacin cewa a sabuwar shekarar Habasha ta 2014 za a samu ingantaccen yanayi, tare da kawo karshen rikicin kasar dake faruwa a halin yanzu.(Ahmad)