logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da furucin ministan tsaron Australiya

2021-09-11 16:12:02 CMG

Kasar Sin na adawa da furucin ministan tsaron Australiya_fororder_0911-Australiya-Faeza

Ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta bayyana adawa mai karfi dangane da furucin da ministan tsaron Australiya Petter Dutton, ya yi game da kasar.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar tsaron Wu Qian ya fitar, ta ce abu ne mai matukar hatsari a rika zuzuta abun da ake kira da “barazanar Sin” da kuma zargin kasar ba tare da tushe ba.

Wu Qian ya ce furucin Dutton, ya bayyana tunaninsa na bangaranci da kaddamar da yakin cacar baka, wanda ba zaman lafiyar duniya da ci gaba da hadin gwiwa kadai ya ke wa barazana ba, har ma da illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin da ma muradun ita kanta Australiar.

Wu Qian ya jadadda cewa, kasar Sin na kiyaye hanyar samun ci gaba cikin lumana da kuma manufar tsaron kasa bisa kariya.

Ya ce kasar Sin ba ta zaman barazana ga kowacce kasa, kuma bunkasa rundunarta na soji baya nufin ta yi hakan ne domin wata kasa. (Fa’iza Mustapha)

Faeza