“Not-to-do List” a fannin yakar ta’addanci
2021-09-11 14:34:24 CMG
A yau ne ake cika shekaru 20 da abkuwar mummunan harin ta’addanci na 9.11 a kasar Amurka. Bayan abkuwar lamarin a shekarar 2001, kasar Amurka ta fara kai hari kasar Afghanistan, bisa fakewa da yakar ta’addanci. Sai dai zuwa yanzu bayan da kasar Amurka ta kashe dala fiye da triliyan 2, da asarar rayukan sojojin kasar fiye da 2000, ta fahimci cewa, ba za ta iya ci gaba da yakin ba. Don haka ta janye sojojinta daga Afghanistan, inda suka haddasa wani yanayi mai matukar muni ta fuskar jin kai: Inda ta lalata kasar, tare da halaka ‘yan Afghanistan fiye da dubu dari daya. Ko da yake kasar Amurka ta yi ikirarin cewa, ta cimma burinta a yayin da take aiwatar da yake-yake a Afghanistan, amma ainihin sakamakon da aka samu ya nuna yadda kasar ta sha kunya a fagen dagar “yaki da ta’addanci” a Afghanistan.
Hausawa su kan ce, “Gani ga wane ya isa wane tsoron Allah.” Yanzu bari mu duba wane irin darasi za mu iya koya daga faduwar totowa da kasar Amurka ta yi a kasar Afghanistan, kana wadanne abubuwa ne ya kamata a kiyaye a yayin da ake neman dakile ta’addanci.
Da farko, bai dace a rika fakewa da batun yaki da ta’addanci don neman cimma wasu muradu ba.
Aikin “yakar ta’addanci” da kasar Amurka ta yi a kasar Afghanistan ya shafi burika daban daban: Tana so ta rushe kungiyar Al-kaida, tana kuma neman hambarar da gwamnatin kasar Afghanistan, da mallakar kasar don neman samun fifiko a fannin takarar siyasa. Wannan kwadayi na kasar Amurka tamkar caca ce, ta hanyar kaddamar da yaki a Afghanistan. Sai dai aikace-aikacenta na rashin adalci sun fusata jama’ar kasashe daban daban. Hakika kasar Amurka ba ta yi nasara ba a lokacin.
Na biyu, aikin yakar ta’addanci na bukatar yin mu’ammala tsakanin bangarori daban daban, da magance yin amfani da karfin tuwo.
Kasar Amurka ta dogaro kan karfinta a fannonin tattalin arziki da aikin soja, inda take ta da yake-yake a kasashe daban daban ba tare da tsoron komai ba. Amma ko da yake tana da kudi, aikin yaki ma ya yi mata wahala. A karshe dai, ta kashe makudan kudade da asarar rayukan mutanenta da yawa, amma wace riba ta samu? Illa kawai kin amincewa da kiyayya da jama’ar kasar Afghanistan, da kusan dukkan Musulmai na kasashe daban daban suke nuna mata. Me ya sa kasar Amurka ba ta iya yin shawarwari tare da Taliban don daidaita matsalar ta’addanci wasu shekaru 20 da suka wuce ba? Zuwa yanzu, bayan da ta sha kunya, ba yadda za ta yi, ban da zama a kan teburin shawarwari tare da Taliban. Sanin kowa ne cewa, ba kowane batu ne, za a iya warware su ta hanyar karfin tuwo ba. A karshe dai ana bukatar daidaita batutuwan ta hanyar shawarwari da mu’ammala.
Na uku, a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, maimakon daukar matakan radin kai.
Yadda kasar Amurka ta sha kunya a yakin da ta yi a Afghanistan ya nuna cewa, zamani na yin babakere a duniya ya riga ya wuce. Idan har ana son yin yaki da ta’addanci, dole ne a dogaro kan hadin gwiwar kasashe daban daban, inda za su yi musayar ra’ayoyi don cimma daidaito, daga baya su dauki matakai a wurare daban daban a lokaci guda, ta yadda za a iya toshe hanyar tsira ta ‘yan ta’adda. A wannan fanni, kasashen yammacin Afirka za su iya zame wa kasar Amurka abin koyi. A shekarun nan, kasashen Najeriya da Nijer da Kamaru da dai sauransu sun kafa hadaddiyar runduna don dakile dakarun Boko Haram a wuraren dake dab da kan iyakokinsu, tare da cimma dimbin nasarori. Kana a nata bangare, kasar Sin ita ma ta dukufa wajen kulla huldar hadin gwiwa a bangaren aikin dakile ta’addanci tare da kasashe makwabtanta, inda har ma ta kira taron ministocin waje na dukkan kasashe makwabtan kasar Afghanistan a kwanan baya, don tabbatar da hadin kansu a kokarin kawar da ta’addanci a yankunansu. Ta haka za mu iya ganin cewa, samun hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban, wata hanya ce mai dacewa a fannin yakar ta’addanci, wadda ya kamata kowa ce kasa ta bi hanyar a nan gaba. Sai dai kasar Amurka ita kadai na ci gaba da kin manufar hadin gwiwa da saura, ganin yadda har yanzu take nuna fuska biyu a fannin yakar ta’addanci, inda ta ki sanya kungiyar dake neman ballewar Xinjiang daga kasar Sin ta ETM cikin jerin sunayen kungiyoyin ta’addanci.
Na hudu, ya kamata a daidaita matsala daga tushe, maimakon kai hari kan kungiyoyin ta’addanci kawai.
Kasar Amurka ta yi kokarin jefa boma-bomai kan ‘yan ta’adda dake Afghanistan, har ma ta kai hari ba tare da bambanta ‘yan ta’adda da fararen hula wadanda ba su san hawa ba balle sauka. Kana ta kashe babban abokin gabanta Usman Bin Laden. Duk da haka, kungiyar Al-Kaida na ci gaba da kasancewa, har ma an fara samun wasu sabbin kungiyoyin ta’addanci irinsu ISIS. Abin da ya fi batanci ga kasar Amurka shi ne, ko da yake ta kwashe shekaru 20 tana kokarin kashe ‘yan ta’adda gami da fararen hula a kasar Afghanistan, amma a kwanakin baya, wata kungiyar ta’addanci ta samu nasarar kai harin kunar bakin wake kan sojojin Amurka, inda har ta halaka sojojin Amurka dake kokarin janyewa daga Afghanistan a lokacin. Ta wannan za mu iya ganin cewa, kashe-kashe da kasar Amurta ta yi ba su da nasaba da ainihin dalilin da ya sa ake samun matsalar ta’addanci. Idan ba a raya tattalin arziki, da kawar da tsattsauran ra’ayi ba, kana aka dogaro da nuna karfin tuwo kawai, to, za a gamu da matsalar da kasar Amurka ke fuskanta, wato za a samu karuwar kungiyoyin ta’addanci a kai a kai. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Najeriya ke bukatar yin afuwa ga ‘yan Boko Haram da suka mika wuya, da koya musu wasu sana’o’i na dogaro da kai. Wannan wani dalili ne da ya sa aka kafa wasu makarantu na koyar da sana’o’i a jihar Xijiang ta kasar Sin, inda aka taimaki wasu mutane kawar musu da tsattsauran ra’ayi, da koya musu fasahohi na sana’a, don sake komawa cikin al’umma.
Yadda kasar Najeriya da kasar Sin suke kokarin hadin gwiwa da kasashe makwabtansu, ya nuna wani nagartaccen yanayi da ake ciki a fannin yakar ta’addanci a duniya, inda ake zama tsintsiya madaurinki daya. Sa’an nan watakila ya kamata mu gode ma kasar Amurka, ganin yadda ta kwashe shekaru 20 tana kokarin aikata kurakurai, tare da gabatar ma kasashe daban daban da wani “Not-to-do List”, wato abubuwan da ya kamata a yi kokarin magance su yayin da ake yaki da ta’addanci. (Bello Wang)