logo

HAUSA

Dole ne Amurka ta canja manufarta kan Sin idan tana son kyautata hulda tsakanin sassan biyu

2021-09-10 20:54:17 CRI

Dole ne Amurka ta canja manufarta kan Sin idan tana son kyautata hulda tsakanin sassan biyu_fororder_中美-1

Yau da safe ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta wayar tarho bisa gayyatar da ya yi masa, inda shugabannin biyu suka yi musanyar ra’ayoyi kan abubuwan da suka jawo hankalin sassan biyu.

Wannan ne karo na biyu da shugabannin biyu suka tattauwa ta wayar tarho, bayan watanni bakwai, yayin zantarwarsu, shugaba Xi ya bayyana cewa, “Yadda ake kyautata huldar dake tsakanin kasar Sin da Amurka ba zabin sassan biyu ba ne, batu ne da ya zama wajibi sassan biyu su daidaita.”

A halin yanzu, dalilin da ya sa huldar dake tsakaninsu ta shiga mawuyancin yanayi shi ne yadda gwamnatin Amurka ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba, da yadda take daukar matakin da bai dace ba domin matsa wa kasar Sin lamba, a don haka idan Amurka tana son kyautata huldar dake tsakaninta da kasar Sin, dole ne ta canja manufar da take aiwatarwa kan kasar Sin, ta daina mayar da kasar Sin a matsayin kalubale ko abokiyar gaba, haka kuma ta daina gurgunta ikon mullki da tsaro da kuma moriyar ci gaban kasar Sin.(Jamila)