logo

HAUSA

Tian Fugang ya cimma burinsa na halartar gasar wasannin Olympics ta nasakassu

2021-09-09 20:00:00 CRI

Tian Fugang ya cimma burinsa na halartar gasar wasannin Olympics ta nasakassu_fororder_0909-tian-1

Koda yake Tian Fugang bai samu lambar yabo a gasar wasannin Olympics ta nakasassu ba, amma yana jin dadi domin ya cimma burinsa na halartar gasar wasannin Olympics ta nakasassu wanda ya tsara tun shekaru 13 da suka gabata.

Babbar girgizar kasa da ta abku a birnin Wenchuan ta kawo babban canji ga rayuwar Tian Fugang, a sakamakon bala’in, Tian Fugang mai shekaru 22 da haihuwa wanda yake aiki a matsayin ma’aikacin gyara injuna ya ji rauni mai tsanani, har bai iya tafiya da kafafunsa.

A lokacin, Tian Fugang har ya fara tunanin kashe kansa, idan ya waiwayi lokacin baya, ya ce, ya san ba zai iya tsayawa da kafarsa ba, da yin rayuwar guragu a nan gaba, ba ya jin dadi, ya ce rayuwarsa bata da amfani.

Bisa goyon bayan da iyalansa suka nuna masa, Tian Fugang ya ziyarci cibiyar taimakawa masu fama da rauni a sakamakon girgizar kasa don samun sauki ta asibitin Huaxi na lardin Sichuan, inda ya koyi yadda ake tashi daga gado zuwa kujerar guragu, da yin tafiya da guragu, har ya hau mataki kan guragu, ya iya sosai kan guragu. Amma ya san wadannan ayyuka ba su ne mafi wuya a gare shi ba, ya kamata ya samu sauki a halin zuciyarsa.

Yayin da yake kokarin koyon fasahohin yin amfani da kujerar guragu, masu koya masa fasahohin sun gano cewa Tian Fugang ya shaida kwarewarsa a kan amfani da kujerar guragu. Wani likita ya gayawa Tian Fugang cewa, yana tsammani Tian Fugang zai zama wani dan wasa mai kyau a nan gaba. Maganar likitan ta burge Tian Fugang sosai.

Tian Fugang ya bayyana cewa, bai taba tunanin zai zama dan wasa ba, amma ya yi tunanin ya kamata ya yi gwaji kan wasan, ana bukatar wani buri a rayuwarsa.

A shekarar 2008, Tian Fugang ya yi hira da dan jarida game da burinsa cewa, yana son zama wani dan wasa, zai halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu a wata rana.

A watan Afrilun shekarar 2009, bisa taimakon gwamnati da kafofin watsa labaru, Tian Fugang ya samu damar yin gwajin horaswa a kungiyar wasan harbe-harbe ta nakasassu ta lardin Sichuan, mai horaswa Wang Ping ta yi tsammani cewa, yana da kwarewa kan wasan, idan yana iya kwantar da hankali, zai samu babban ci gaba kan wasan, don haka tana kiyaye shi a kungiyar.

Ya yi horaswa sau da dama, kamar daga bindiga, daukar saiti, yin harbi, ajiye bindiga, sake daga bindiga, kamar hakan sau fiye da dubu daya a kowace rana. A filin wasan harbe-harbe, Tian Fugang ya kwantar da hankalinsa. Don cimma burinsa, ya yi namijin kokari kan horaswa.

Amma raunin da ya ji ya a shi gane wuyar da ‘yan wasan nakasassu su kan fuskanta. Ya ce, domin ya sanya rigar wasan yin harbe-harbe da yin horaswa kan kujerar guragu a dogon lokaci, a kan samu ciwo kan duwawu, a kan gano shi bayan da ya fara jin ciwo. Ya ce, akwai wuya  wajen samun sauki a bisa ga yanayin ranunin dake jikinsa, ana bukatar karin lokacin domin samun sauki kan ciwon. A shekarar 2010, ya kamu da irin ciwon, an kwashe shekaru 3 kafin samun saukin. Bayan hakan, ya sake kamuwa da ciwon har sau biyu, wanda ya kawo babbar illa ga horaswarsa.

Tian Fugang ya cimma burinsa na halartar gasar wasannin Olympics ta nasakassu

Koda yake, Tian Fugang ya fuskanci mawuyancin hali, amma bai yi watsi da wasan da kuma burin da yake son cimmawa ba, ya kiyaye yin kokari don cimma burinsa a wasan. A shekarar 2010, Tian Fugang ya halarci gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu ta Asiya a birnin Guangzhou na kasr Sin, wannan ne karo na farko da ya yi wasan a dandalin nahiyoyin duniya. Bayan hakan, ya ci gaba da yin kokari da inganta kwarewarsa a wasan, da samun lambobin yabo a gasannin kasar Sin da ma na kasashen waje. A shekarar 2019, Tian Fugang ya samu lambar zinari a gasar wasan harbe-harbe ta nakasassu ta duniya da aka gudanar da birnin Sydney na kasar Australia, wannan ne karo na farko da ya cimma zakara a wasan a duniya.

A farkon shekarar 2019, Tian Fugang ya samu cikakkun maki a gasannin wasan harbe-harbe na nakasassu na duniya, ya samu iznin shiga gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta birnin Tokyo. Ya bayyana cewa, yana jin farin ciki sosai a lokacin, burinsa na halartar gasar wasannin Olympics na nakasassu da ya yi kokarin cimma shi har na tsawon shekaru fiye da 10 ya cika.

Koda yake, Tian Fugang bai samu lambobin yabo a gun gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Tokyo ba, amma ya ji gamsuwa kan wasan da ya yi, ya ce domin ya samu ci gaba a sakamakon halartar gasar.

Tian Fugang ya ce, rayuwar dan Adam ta yi kamar gasa, ba abu ne mai yiwuwa ba a kiyaye samun nasara a kowane lokaci. Amma idan wani ya kiyaye yin kokari, zai cimma burinsa a wata rana. Halartar gasar wasannin Olympics ta nakasassu tana da babbar ma’ana ga Tian Fugang, wadda ya shaida cewa, kokarin da ya yi a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata bai tashi a banza ba, kana ya kara yin imani cewa, idan an kiyaye yin kokari, to za a cimma buri.

Wasan harbe-harbe ya canja rayuwar Tian Fugang, ya kara yin imani da kansa da cimma burinsa ta hanyar kokarinsa, kana ya samu soyayya a kungiyar wasan harbe-harbe. Shi da ‘yar wasan kungiyar Tao Lan suna kaunar juna, sun yi aure a shekarar 2012, yanzu suna da ‘ya mai shekaru 8 da haihuwa. Lokacin da yake hira da matarsa da ‘yarsa, yakan yi murmushi, yana ji dadin zaman rayuwasa a yanzu.

Tian Fugang ya ce, rayuwa ba za ta yi watsi da kowane mutum ba, idan mu ba mu yi watsi da rayuwarmu ba, to za mu ji dadin zaman rayuwarmu a nan gaba.(Zainab)