logo

HAUSA

Shugabannin Afrika sun jaddada aniyar ajandar samar da abinci

2021-09-09 10:13:36 CRI

Shugabannin Afrika sun jaddada aniyar ajandar samar da abinci_fororder_0909Africa-Ahmad

Shugabannin kasashe da hukumomin gwamnatocin kasashen yankin Hamadar Afrika sun jaddada aniyarsu game da ajandar samar da abinci a matsayin wani bangare na shirin farfadowa daga annobar COVID-19.

Da suke gabatar da jawabai a wajen taron kolin dandalin bunkasa ayyukan gona na Afrika (AGRF) na shekarar 2021, wanda ke gudana a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, shugabannin sun ce, akwai bukatar a sauya salon ayyukan noma domin bunakasa samar da abinci, da tabbatar da inganta samar da sinadarai masu gina jiki da bunkasa hanyoyin samun kudaden shigar mazauna karkara yayin da nahiyar ke fadi-tashin neman farfadowa daga mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar.

Kasar Kenya ce ke karbar bakuncin taron kolin na AGRF na 2021 daga ranakun 7 zuwa 10 ga watan Satumba, mai taken “Hanyoyin farfadowa da karfafa tsarin samar da abinci". (Ahmad Fagam)