logo

HAUSA

‘Yan Siyasar Amurka Da Birtaniya Sun Nuna Fuska Biyu Kan Harkokin Hong Kong

2021-09-09 15:44:48 CRI

‘Yan Siyasar Amurka Da Birtaniya Sun Nuna Fuska Biyu Kan Harkokin Hong Kong_fororder_微信图片_20210909152320

Daga CRI HAUS

Daga daren jiya zuwa wayewar garin yau, ministan harkokin wajen kasar Birtaniya Dominic Raab, da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, sun ba da bayani kan shafin yanar gizo na sada zumunta don tsoma baki kan batun cafke mambobin wata kungiya da ‘yan sandan yankin Hong Kong na kasar Sin suka yi bisa doka, sun shafa bakin fenti na cewa, wai matakin da ‘yan sandan suka dauka ya sabawa shari’a da doka da yin watsi da bambamcin ra’ayi da sauransu. Irin wadannan maganganu sun nuna goyon bayan ‘yan a-ware da bayyana cewa, lalle wannan kungiya tana karkashin jagorancin wasu kasashe, abin da ya sheda cewa, akwai wajabcin ‘yan sandan Hong Kong su dauki matakin mai dacewam sa’an nan wasu ‘yan siyasar Birtaniya da Amurka sun nuna fuska biyu da kuma rashin sahihanci.

Bai kamata ‘yan siyasar Birtaniya da Amurka su aikata hakan kan batun Hong Kong ba, dole ne su fahimci hakikanin halin da ake ciki da yin tafiya daidai da lokaci, su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin da yadda ake tafiyar da harkoki bisa doka a yankin Hong Kong. Idan ba haka ba, Sin da jama’arta za su mai da martani. (Amina Xu)