logo

HAUSA

Yadda Amurka ke nuna fuska biyu kan yaki da ta’addanci yana kawo illa ga ita kanta Amurka da sauran kasashe

2021-09-08 20:52:45 CRI

Yadda Amurka ke nuna fuska biyu kan yaki da ta’addanci yana kawo illa ga ita kanta Amurka da sauran kasashe_fororder_amurka

A jajiberin cika shekaru 20 da aukuwar harin ranar 11 ga watan Satumba, a hannu guda kuma yakin da Amurka ta yi a kasar Afghanistan bai yi nasara ba.

A watan Oktoban shekarar 2001, Amurka ta tura sojojinta zuwa Afghanistan bisa fakewa da “yaki da ta’addanci”, duk da cewa, sojojin Amurka sun harbe madugun kungiyar Al Qaeda Bin Laden har lahira a shekarar 2011, amma hare-haren ta’addanci da suka faru a fadin duniya suna karuwa matuka.

Dalili kuwa shi ne, Amurka tana fakewa da batun yaki da ta’addanci ne don kare moriyar kanta kawai, haka kuma ta kasa kula da bukata da moriya na sauran kasashe, inda take amfani da fuska biyu kan ayyukan ta’addanci.

Hakika tun farkon da Amurka ta tura sojoji zuwa kasashen Afghanistan da Iraki da sauran kasashe, ‘yan siyasar kasar sun nuna yunkurinsu na hada aikin yaki da ta’addanci da nuna fin karfi da murkushe mulkin sauran kasashe waje daya, duk wadannan sun kara tsananta rikici da tashin hankali a kasashe da yankunan da abin ya shafa.

A don haka ya zama wajibi Amurka ta yi watsi da matakin da bai dace ba da ta dauka, ta hanyar amfani da fuska biyu kan yaki da ta’addanci, in ba haka ba, illar hakan za ta koma kanta.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)