Ya kamata Amurka ta hada kai da kasar Sin don yakar COVID-19
2021-09-08 19:05:39 CRI
A yayin da wani sabon nau’in COVID-19 ke ci gaba da addabar sassan duniya, a hannu guda kuma alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar ya nuna cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 40.
Wannan ya kara nuna cewa, Amurka ce kasar da annobar ta fi kamari, inda ta fi kowace kasa a duniya yawan mutunen da suka kamu da kuma wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar, kana ita ce ke da sama da kashi 18 bisa 100 na dukkan yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya, kana tana da kusan kashi 14 cikin dari na yawan mutanen da cutar ta halaka a duniya
Yadda jagororin kasar Amurka suka gaza wajen daukar matakan dakile wannan annoba, ya nuna cewa, zabi mafi kyau ga Amurka shi ne ta saurari fata da ra’ayoyin al’ummar duniya da idon basira, ta hada kai maimakon yin fito na fito, ta kasance mai goyon baya maimakon yiwa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da ma aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 zagon kasa, ko neman bata sunan wata kasa, don cimma wani buri na siyasa.
Shi ma Jeffrey Sachs, shugaban kwamitin COVID-19 na mujallar kiwon lafiya ta “The Lancet” ta kasar Burtaniya, ya bayyana a kwanakin baya cewa, duniya ba ta dauki matakan da suka dace game da annobar COVID-19 ba. Dalili shi ne, Amurka ta gaza hada kai da kasar Sin don lalubo bakin zaren magance wannan batu a duniya baki daya.
Masharhanta na kara nanata cewa, duk masu neman siyasantar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, hakika suna tafka babban kuskure ne ga aikin yaki da annobar. Kamata ya yi su martaba matakai na kimiya da shaidu na zahiri. Masanin kwayoyin cututtuka na Najeriya kana shugaban kwamitin kwararru na kasar dake bibiyar cutar COVID-19 Oyewole Tomori, ya bayyana cewa kamata ya yi a daina siyasantar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar Covid-19, maimakon haka, a mayar da hankali kan shaidun kimiyya na zahiri.
Ya kuma yi imanin cewa, a halin yanzu kamata ya yi a yi watsi da tunanin da wasu ke yi wai, kwayar cutar ta bulla ne daga dakin bincike, har sai an samu kwararan shaidu dake tabbatar da hakan, amma idan har hakan ya zama wajibi, kamata ya yi a gudanar da aikin binciken a duniya baki daya, karkashin jagorancin WHO, ba kuma tare da matsin lamba daga Amurka ba. Ta kuma hada kai da kasar Sin, maimakon neman kakaba mata ra’ayinta. Sanin kowa ne cewa, kasar Sin dai ta dauki managartan matakai wajen nasarar dakile annobar, baya ga gudummawar da take bayarwa a yaki da wannan annoba a dukkan fannoni. A don haka, ya kamata duniya ta koyi darussa masu yawa daga irin matakan da kasar Sin ta dauka, don ganin an kawo karshen wannan annoba. (Ibrahim Yaya)