logo

HAUSA

A kara kulla alakar kud-da-kud tsakanin kasa da kasa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”

2021-09-08 11:10:30 CRI

A kara kulla alakar kud-da-kud tsakanin kasa da kasa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”_fororder_src=http---mstatic.gzstv.com-media-images-2019-04-23-5cDnh4i_FMGd&refer=http---mstatic.gzstv

Yau shekaru 8 ke nan da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da babbar shawarar raya “ziri daya da hanya daya” tare da kasashen da ke kan hanyar siliki.

Yayin da suke tinkarar annobar COVID-19, kasashen dake bin tsarin shawarar sun taimaka wa juna gami da haye wahalhalu tare, wadanda suka karfafa zukatan kasashen duniya wajen samun nasara a kan cutar, baya ga babbar gudummawar da suke bayarwa ga hadin kan kasa da kasa don yaki da cutar da ma farfadowar tattalin arzikin duniya.

A farkon rabin shekarar bana, yawan hajojin da aka aika ta layin dogo a tsakanin Sin da Turai ya karu da kaso 41 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, sa’an nan yawan jarin da aka zuba wa kasashen kai tsaye a fannonin da ba su shafi sha’anin kudi ba ya karu da kaso 19.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Haka zakila, a cikin wadannan shekaru 8 da suka gabata, jimillar kudin cinikayyar da ke tsakanin Sin da kasashen ta zarce dala triliyan 9.2, yawan jarin da masana’antun kasar Sin suka zuba wa kasashen kai tsaye ya zarce dala biliyan 130. Lamarin da ya sa “ziri daya da hanya daya” ya zama dandalin hadin kan kasa da kasa mafi girma a duniya.

Rahotannin bankin duniya na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2030, ana sa ran mutane miliyan 7.6 daga kasashen duniya za su fita daga kangin talauci mai matukar tsanani, kana miliyan 32 za su fita daga talauci a karkashin inuwar shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron dandalin tattalin arzikin duniya na Davos da sauran manyan taruka a bana, ya gabatar da cewa, dukkan kasashen dake da sha’awar bin tafarkin shawarar “ziri daya da hanya daya”, za su iya sa hannu a ciki don samun maradu tare. Burin raya shawarar shi ne a samu ci gaba da nasara tare domin a samar da kyakkyawar makoma tare. (Kande Gao)