Xiangyang: Tsohon birnin dake tafiya da zamani
2021-09-08 09:06:23 CRI
A kwanakin baya, abokiyar aikinmu Fa’iza Mustapha ta kai ziyara birnin Xiangyang na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, wani daddaden birni ne da ya samo asali shekaru kimanin dubu shida kafin haihuwar annabi Isa AS. A cikin shirin yau, Fa’iza ta kawo mana abubuwan da ta gane da idonta a birnin.
Xiangyang ya kasance birnin da ya fuskanci yake-yake a dauloli 3 na kasar Sin, kana birnin ne dake tsakiyar birane hudu da katafaren Kogin Han ya ratsa. Kasancewarsa tsohon wuri, bai sa mahukunta sun yi kasa a gwiwa wajen raya shi ba. Maimakon zamanantarwa kadai, sai suka dukufa wajen harbin tsuntsaye biyu da dutse guda, inda aka yi ta kokarin raya al’adun gargajiya ta hanyar kiyaye kayayyakin wuraren tarihi da aka yi gado, a daya hannun kuma, ake ci gaba da zamanatar da shi.
A ziyarar yini guda da Fa’iza Mustapha ta yi, lallai ta samu damar ganewa idonta wasu daga cikin ci gaban da wannan birni ya samu kawo yanzu.
Misali, dukufar da ake yi wajen raya tattalin arzikin birnin ya zama abun burgewa matuka, lamarin da ya kai alkaluman GDPnsa da ya tsaya kan kusan yuan biliyan 36.8 a shekarar 2000, ya karu zuwa yuan biliyan 481.28 a shekarar 2019. Kamar yadda ake cewa, noma tushen arziki, to haka batun yake ga Xiangyang, inda aikin gona ya kasance daya daga cikin ginshinkan arzikinsa, ta hanyar noman ganyen shayi da gero har ma da auduga da sauran wasu kayan marmari da lambu. Haka kuma ci gaban da birnin ke samu, ya kai shi ga shiga shirin gwamnatin kasar Sin na raya tattalin arzikin yankunan dake kewaye da kogin Yangtze.
Wani abun birgewa shi ne, yadda ya yi suna a bangaren kere keren injuna daban daban, lamarin da ke kara zamantar da shi da kuma bunkasa tattalin arzikinsa. Hakika namijin kokarin da aka dukufa ana yi cikin wannan birni, ya sa ya zama cibiyar da samar motoci har ma da gwajinsu a kasar Sin, wanda kuma ke da hadin gwiwa da kamfanonin kera motoci na kasashen waje. Ba za a samu ci gaba ba tare da an yi kyakkywan tsari game da burin da ake son cimmawa ba, wanda tunani ne irin na Sinawa da a kullum shugaban kasar Sin Xi Jinping ke kira da su ci gaba da dabbakawa. Kuma bisa wannan ne, ake da burin raya wannan birni zuwa sabon birnin kera motocin zamani na Sin, haka kuma wurin saka tufafi da amfani da sabon makamashi da kuma cibiyar bunkasa harkokin sararin samaniya. A ganin Fa’iza, dukkan wadannan ba sabbin ayyuka ba ne, haka kuma ba abubuwa ne da ba za a iya cimma su ba, domin tuni an riga an yi shimfida an kuma kafa tubalin, don haka, Fa’iza ta amince da cewa, cikin shekaru kalilan masu zuwa, wannan buri zai zama daga cikin tarihin ci gaban Xiangyang , inda kuma za a tsara wasu sabbin tsaruka. (Fa’iza Mustapha, Ibrahim Yaya)