logo

HAUSA

Cinikin Yanar Gizo Na Taimakawa Kasashen Afrika Shiga Kasuwar Kasar Sin

2021-09-08 15:58:54 CRI

Cinikin Yanar Gizo Na Taimakawa Kasashen Afrika Shiga Kasuwar Kasar Sin_fororder_1293086572728811567

Daga Amina Xu

Na taba zantawa da Leo Nwaigwe dan Najeriya dake ciniki a birnin Yiwu na lardin Zhejiang, a shekarar 2016, inda ya gaya min cewa, a lokacin da ya fara ciniki ta yanar gizo, ya samu takardun neman sayen kaya daga Alibaba. Ya ce, cinikin yanar gizo ya saukaka masa yin ciniki, na samu kayayyaki masu kyau ta Intanet da tuntubar karin masu sayayya, abin da ya nuna cewa, za a samu karin riba.

Leo Nwaigwe yana sayar da kayayyakin ado na Sin zuwa Najeriya, ya ce akwai kaya masu kyau a kasashen yammacin Afirka, kamar Shea butter wato man kadanya, wadanda yake son sayar da su a nan kasar Sin.

Shekaru 5 da suka gabata, cinikin yanar gizo na bunkasa cikin sauri, ba shakka Leo yana kara samun ciniki. Ban da wannan kuma, don ingiza kasashen Afrika su kara shiga kasuwar Sin, ya sa kasar Sin ta bullo da bikin baje kolin kayayyakin Afrika na tsawon watanni 3 karkashin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na shekarar 2021 a ranar 6 a nan birnin Beijing. Ba shakka matakin zai baiwa ‘yan kasuwar Afrika kamar Leo, wani sabon dandali na yayata kayayyakin Afrika, kuma Man kadanyan da ya sayar, ya yiwu zai samu karbuwa a kasuwar kasar Sin.

Leo ya shaida min cewa, ba da jimaba ba da ya fara yin ciniki ta yanar gizo ba, ya samu zarafi mai kyau, wato birnin Yiwu ya kara karfin raya cinikin yanar gizo tare da yin kwaskwarima kan harkokin cinikin kasa da kasa a shekarar 2011, wanda ya gyara tsarin sayen kayayyaki ta kasuwanni, inda aka tara kayayyaki iri daban-daban ta manyan kwantenoni da jami’an kwastan za su bincika a lokaci guda, matakin da ya saukakawa ‘yan kasuwa matukar. Haka kuma matakin ya jawo hankali ‘yan kasuwa daga Afrika da yankin gabas ta tsakiya masu yawa, wadannan ‘yan kasuwa, sun kara shiga kasuwar kasar Sin ta hanyar yanar gizo. A cibiyar cinikin kasa da kasa dake birnin Yiwu, ana baje kolin kayayyakin kasa da kasa, musamman ma kayayyakin kasashen Afrika, kuma ‘yan kasuwar Sin suna iya zaben kayan da suke so ta yanar gizo.

Mai dandalin cinikin yanar gizo na TOFA wato Trade of Africa a Turance Madam Uju ta taba shiga shirin taimakawa masu kamfanoni da Alibaba ya gabatar, bayan ta kammala horo a birnin Hanzhou, Uju ta hada kai da masu neman kafa kamfanoni na kasa da kasa, don taimakawa manoman kasashe marasa ci gaba, ciki har da Togo wajen sayar da kayayyakin amfanin gona ta yanar gizo. Masu shiga shirin da Sin ta gabatar, suna amfana da fasaha ta yanar gizo, kuma sun ganewa idanunsu girman kasuwar kasar Sin. An yi imani cewa, ‘yan kasuwar Afrika, za su shiga kasuwar kasar Sin bisa fasahar da suka koya daga Sin ta dandalolin cinikin yanar gizo.

Kamar yadda shugaban tawagar jakadun Afrika dake kasar Sin kana jakadan Kamaru dake kasar Sin Martin Mpana ya nuna cewa, bikin baje koli da aka shirya a wannan karo, mataki ne mai muhimmanci wajen daidaita cikini tsakanin Sin da Afrika da kuma kokarin ganin Afirka ta fitar da karin kayayyakinta zuwa kasar Sin. Fasahar yanar gizo ta bude wani sabon babi na dunkulewar duniya baki daya, a don haka, ya kamata kasashen Afrika su amfana da wannan dandali don kara shiga babbar kasuwar kasar Sin. (Amina Xu)