logo

HAUSA

Tabbatar zaman lafiya a duniya, na bukatar sauyin dabaru

2021-09-07 19:14:17 CRI

Tabbatar zaman lafiya a duniya, na bukatar sauyin dabaru_fororder_hoto

"Raya Makoma ta bai daya a shekarar 2021" shi ne taken atisayen wanzar da zaman lafiya da Kasar Sin ta kaddamar jiya Litinin, wanda ya kunshi kasashen Sin Mongolia da Pakistan har ma da Thailand.

A tunanina, wannan gagarumin mataki ne da Sin ta dauka yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye. Rikice-rikicen da suka shafi kabilanci da siyasa da addini na barkewa a sassa daban-daban na duniya, haka zalika masu munanan manufofi ko aikata laifuffuka, na ci gaba da ta da hankalin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Don haka, yayin da ake fuskantar sabbin sauye-sauye, ya kamata duniya ta shiryawa tunkararsu. Har kullum na kan yabawa hangen nesa irin na kasar Sin, yadda a kullum take sanin abun da ya kamata a lokacin da ya kamata. A kan ce, idan rawa ya canza, dole kidi ma ya canza, don haka ne wannan atisaye zai gudana a wani yanayi mai kama da zahiri da dacewa da yanayin kasashe daban-daban. Yadda ake matukar son ganin zaman lafiya, haka ya kamata a ko da yaushe a rika kasancewa cikin shirin ko ta kwana. Rashin atisaye  da canza dabaru ko salon yaki, na daya daga cikin matsalolin da ya sa har yanzu wasu kasashen ke fuskantar rashin nasara a fagen yaki da ‘yan ta’adda ko masu aikata muggan laifuka.

Kasar Sin kasa ce da za a iya kiranta mai cike da zaman lafiya, domin ta riga ta toshe duk wata kafa da bata gari za su iya samu wajen kawo mata tarnaki, don haka daukar darassi daga gareta, ya zama muhimmin abu ga kasashen duniya, musammam kasashe masu tasowa dake fuskantar rikice-rikice da ayyukan ta’addanci.

A matsayinta na kasar da ta fi kowacce bayar da gudunmuwar dakaru ga aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, kasar Sin tana tabbatar da furucinta na kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya da inganta huldar kasa da kasa. Irin wannan atisaye da take shirya, zai kara wayar da kan sojojinta kan halin da kasashe daban-daban suke ciki da kuma yadda za su tunkari duk wani kalubale da za su fuskanta. Wato ba wai sojoji a sunan sojoji kawai take bayarwa ba, sojoji ne da suka cancanci a kirasu da sunan, masu kwarewa da kuma dabaru. Wannan ma alama ce dake nuna kudurinta na kara bada gudunmuwa ga zaman lafiya na bai daya a duniya tare da kara tabbatar da matsayinta na babbar kasar da ta san ya kamata. (Fa'iza Mustapha)