logo

HAUSA

Sin ta kaddamar da atisayen wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa

2021-09-07 10:21:52 CRI

Sin ta kaddamar da atisayen wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa_fororder_d47346ce49fa4a72b637c8cc0608f040

A ranar Litinin kasar Sin ta fara atisayen wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa wanda aka yiwa taken "Raya makoma ta bai daya a shekarar 2021".

Wannan shi ne karon farko da dakarun sojojin kasar Sin suka shirya irin wannan gagarumin atisayen wanzar da zaman lafiya, wanda ya samu halartar dakarun sojoji da suka hada da na kasashen Sin, Mongolia, Pakistan da Thailand.

Kamar dai yadda aka tsara, za a gudanar da shirin ne a bisa hadin gwiwar dakarun tsaron wanzar da zaman lafiya na kasashen, kuma za a gudanar da shirin ne tamkar a filin yaki na zahiri bisa dacewa da tsarin kasa da kasa, da kuma tsarin da kwararrun masana tsaro suka amince da shi.

Masana al’amuran sojojin sun ce, atisayen ya kara bayyana aniyar kasar Sin wajen bayar da cikakkiyar gudunmawa da kuma taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Kasar Sin ita ce kasar da ta fi kowace bayar da taimakon dakarun kiyaye zaman lafiya cikin mambobin kasashe masu wakilcin dindindin a kwamitin sulhun MDD.(Ahmad)