logo

HAUSA

Jagoran juyin mulkin kasar Guinea ya yi alkawarin kafa gwamnatin hadin kan kasa

2021-09-07 10:23:22 CRI

Jagoran juyin mulkin kasar Guinea ya yi alkawarin kafa gwamnatin hadin kan kasa_fororder_1127835205_16309794672361n

A ranar 6 ga watan Satumba, jagoran da ya shirya juyin mulkin kasar Guinea, Mamady Doumbouya, ya gabatar da jawabi bayan tattaunawa da ministocin tsohuwar gwamnatin Shugaba Alpha Conde a fadar shugaban kasar dake Conakry.

Inda Mamady Doumbouya, ya yi alkawarin kafa gwamnatin hadin kan kasa nan da wasu makonni masu zuwa, sai dai ya ce, babu wata muzgunawa da za a yi wa tsoffin ministocin gwamnatin Conde, amma ana bukatar kada su fice daga kasar Guinea. Sannan kuma, Doumbouya ya bukaci kamfanonin hakar ma’adanai na kasar da su dawo bakin aikinsu, kana ya ce za a dage dokar hana fita ga sassan yankin kamfanonin ma’adanan.

Mamady Doumbouya ya kuma bayyana cikin sanarwar da aka watsa ta gidan talabijin din kasar cewa, an sake bude iyakokin kasa da na sama na kasar domin a samu damar gudanar da hada hadar yau da kullum da kuma samun damar gudanar da ayyukan agajin bil Adama.(Ahmad)