logo

HAUSA

An Gabatar Da Bikin Baje Kolin Kayayyakin Afrika Ta Yanar Gizo Na Dandalin Tattaunawar Hadin Kan Sin Da Afrika Na Shekarar 2021

2021-09-07 10:52:42 CRI

An Gabatar Da Bikin Baje Kolin Kayayyakin Afrika Ta Yanar Gizo Na Dandalin Tattaunawar Hadin Kan Sin Da Afrika Na Shekarar 2021_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_spider202033_200_w600h400_20200303_e4c5-iqfqmat7275214&refer=http___n.sinaimg

BY CRI HAUSA

An bude bikin baje kolin kayayyakin Afrika ta yanar gizo na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na shekarar 2021 na tsawo watanni 3 a jiya Litinin a nan birnin Beijing.

Bisa kididdigar da aka bayar, ciniki tsakanin Sin da Afrika a wannan shekara yana samun farfadowa mai inganci. Daga watan Jarairu zuwa Yuli, yawan kudin dake shafar cinikin bangarorin biyu ya kai dala biliyan 139.1, wanda ya karu da kashi 42% bisa na makamancin lokaci na bara. A sa’i daya kuma, kasuwannin Sin na kara bude kofa ga Afrika. A shekarar 2020 yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyakin amfanin gona daga Afrika ya karu da kashi 4.6% bisa na makamancin lokaci na bara, wanda ya samu karuwa a cikin shekaru 4 a jere. A yayin bikin budewa, babban direktan sashen kula da harkokin Afrika na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wu Peng ya ce, Sin tana fatan habaka shigo da kayayyaki daga Afrika, ba ta son rarar kudi daga cinikin Sin da Afrika, don more ci gaban bunkasuwa tare da kasashen Afrika. Wu Peng ya ce,

“Ciniki ta yanar gizo ya ingiza kwaskwarimar al’umma da tattalin arziki da Sin da Afrika ke yi a fannin yanar gizo. Afrika na da albarkatu masu dimbin yawa, ciniki ta yanar gizo na taimakawa Afrika wajen bude kasuwarta ga kasar Sin. Alal misali, Afrika ta kan fitar da waken kofi, yawan kudin da aka samu ta fuskar sha’anin shuka da sarrafa kofi ya kai kashi 1/10. A wajen bikin baje kolin kayayyaki da Sin ke shigo da su daga waje, wasu kamfanonin waken kofi sun shiga dandalin T-Mall na yanar gizo, abin da ya taimakawa Afrika wajen habaka wannan fanni.”

Wu Peng ya nuna cewa, gabatar da wannan biki zai taimakawa masu sayayya na kasar Sin da su sayi kayayyaki masu kyau daga Afrika, musamman ma kayayyakin gona, abin da zai kara kudin shigar manoman Afrika. Wannan biki na baje kolin kayayyakin Afrika a nan kasar Sin ta yanar gizo hadin kan bangarorin biyu ne dake kawo moriyar juna, matakin da ya bayyana ruhin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na hadin kai da cin moriya tare.

Shugaban tawagar jakadun Afrika dake kasar Sin kana jakadan Kamaru dake kasar Sin Martin Mpana ya nuna cewa,

“Muna matukar bukatar tuntubar juna da hadin kai da juna. Ina kira ga masu zuba jari masu zaman kansu na kasar Sin da su zuba jari a Afrika, musamman a fannin samar da manyan ababen more rayuwa ta fuskar sadarwa, ta yadda za a ingiza cinikin Sin da Afrika ta yanar gizo. Kasuwar sayayya ta kasar Sin tana da girma kuma kasuwa ce mai kyau ga kayayyakin Afrika, nahiyar Afrika tana da yawan mutane biliyan 1.2, ita ma wata kasuwa ce mai kyau ta kayayyaki ga masu zuba jari na Sin. Hakan ya sa, ya kamata mu ci gaba da habaka kyakkyawar makomar Sin da Afrika ta bai daya.” (Amina Xu)