logo

HAUSA

An samu babban sakamako yayin bikin hada-hadar hidimomin kasa da kasa na kasar Sin

2021-09-07 20:59:30 CRI

An samu babban sakamako yayin bikin hada-hadar hidimomin kasa da kasa na kasar Sin_fororder_biki

Yau Talata 7 ga wata an rufe bikin hada-hadar hidimomin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2021 wanda aka shafe kwanaki shida aka gudanar a nan birnin Beijing. Alkaluman farko sun nuna cewa, ya zuwa yammacin yau, da misalin karfe hudu, gaba daya an daddale kwangilolin ayyukan da su kai 1672 yayin bikin, adadin da ya zarce na bikin da aka gudanar bara.

A matsayinsa na biki mafi girma a fannin hada-hadar hidimomi a fadin duniya, bikin da aka shirya a nan birnin Beijing ya samar da damar samun ci gaba ga kamfanonin kasashen duniya baki daya, haka kuma ya samar da muhimman dabaru ga kasashen duniya wajen dakile rikicin tattalin arziki sakamakon yaduwar annobar cutar COVID-19.

Kana bikin hada-hadar hidimomi ya kasance dandalin da ya hada kowa da kowa, inda ya taka rawa wajen taimakawa kasashe masu tasowa yayin da ake kokarin daidaita matsalar rashin daidaiton farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ban da haka, abu mafi muhimmanci shi ne, alamar kara bude kofa ga ketare da kasar Sin ta nuna yayin bikin ta kara imani ga kasa da kasa kan yadda za su farfado da tattalin arziki wanda ya gamu da matsala.

Duk da cewa an rufe bikin, amma za a ci gaba da gudanar da bikin ta kafar yanar gizo, saboda kasar Sin tana son shirya bikin hada-hadar hidimomi mai dorewa wanda ba za a rufe shi ba har abada, dalili shi ne, kasar Sin ba za ta daina aiwatar da manufar bude kofa ba har abada, kuma ba za ta daina yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin samun moriya tare ba har abada.(Jamila)