logo

HAUSA

ECOWAS ta yi Allah wadai ta juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea

2021-09-06 20:14:20 CRI

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta fitar da wata sanarwar bayan taro, inda a cikinta ta bayyana cewa, tana Allah wadai da babbar murya kan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi jiya a kasar Guinea

Haka kuma ECOWAS, ta bukaci da a kare lafiyar shugaban Guinea Alpha Conde, kana a gaggauta sakinsa da ma dukkan wadanda ake tsare da su ba tare da gindaya wani sharadi ba.

A wannan rana, ita ma gwamnatin Najeriya, ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ta Guinea, inda ta bayyana takaici kan yadda aka keta yarjejeniyar kungiyar ECOWAS game da tsarin demokiradiya da shugabanci na gari a Jamhuriyar Guinea.(Ibrahim)