logo

HAUSA

Cristiano Ronaldo Ya Dawo Manchester United

2021-09-06 10:50:52 CRI

Cristiano Ronaldo Ya Dawo Manchester United_fororder_src=http___zugou.oss-accelerate.aliyuncs.com_public_2020_05_28_159063842531455.png&refer=http___zugou.oss-accelerate.aliyuncs

Cristiano Ronaldo Ya Dawo Manchester United

Shafin kungiyar kwallon kafa na Manchester United ya tabbatar da dawowar dan wasa Cristiano Ronaldo kungiyar, bayan ya shafe shekaru da barin kungiyar. Ronaldo ya zauna a kungiyar Madrid tsawon shekaru, inda daga bisani ya koma kungiyar Juventus, a yau kuma ya dawo tsohuwar kungiyar shi ta Manchester United.

Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar Manchester City ta fasa sayen Ronaldo din daga kungiyar Juventus, a yau kungiyar ta Manchester United ta shiga cinikin dan wasan, kuma ta saye shi cikin kankanin lokaci. A jiya ne Ronaldo ya bayyanawa kociyan Juventus cewar shi kam zaman shi ya kare a kungiyar ta Juventus.

Watakila Messi Ya Fara Wasa A PSG A Wannan Makon

Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa watakila kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta saka sabon dan wasanta Lionel Messi ya buga mata wasa a karon farko, tun bayan da ya koma kungiyar a kakar bana.

 

Ranar Lahadi PSG za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Reims a wasan mako na hudu a gasar Faransa ta Ligue 1 ta bana kuma PSG ta ci dukkan wasa ukun da ta buga a bana a Ligue 1, ita ce kan gaba a teburi, duk da Neymar da Messi ba su buga mata wasan ba.

Watakila lokaci ya yi da ya kamata kociyan kungiyar Mauricio Pochettino ya fara saka kyaftin din Argentina, wanda rabon da ya buga wasa tun bayan kofin Copa del Rey da suka lashe a Brazil a bana.

Messi wanda ya koma Faransa da buga wasa a bana, bayan da Barcelona ta fada cikin matsin tattalin arziki, yana atisaye a PSG, wadda ta gabatar da shi gaban magoya bayanta tun a farkon wannan watan.

Cikin sababbin ‘yan wasan da PSG ta dauka a bana, Gianluigi Donnarumma ya yi zaman benci a ranar Juma’a a wasan da ta doke kungiyar Brest 4-2 ya yin da Achraf Hakimi da kuma Georginio Wijnaldum sun buga wa PSG dukkan fafatawa ukun da ta yi a Ligue 1 na bana.

Kawo yanzu Messi da mai tsaron ragar tawagar Italiya, Donnarumma ne ba su buga wa PSG wasa ba, cikin sabbin ‘yan kwallon da ta dauka a bana, sannan wani dan kwallon da shi ma bai fara yi wa PSG wasa ba, shi ne, Sergio Ramos, wanda ke jinya da ba a fayyace lokacin da zai murmure ba.

Messi ya koma Paris St Germain, bayan shekara 21 da ya yi a Camp Nou, bayan da Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki kuma tun makon da ya wuce shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sanar cewar bashi ya yi wa kungiyar katutu da ya kai Fam biliyan 1.35.

Matsin tattalin arzikin da Barcelona ta fada ne ya sa ta kasa tsawaita kwantiragin Messi, wanda ya amince da rage rabin albashin sa kuma tuni kyaftin din tawagar Argentina ya saka hannu kan yarjejeniyar kakar wasa biyu a kungiyar ta PSG da sharadin za a iya tsawaitata kaka daya nan gaba.

Ko Manchester City Za Ta Hakura Da Dan Wasan Gabanta?

Tuni dan wasa Harry Kane ya bayyanawa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham cewa zai ci gaba da zama a kungiyar wanda hakan ya kawo karshen cece-kucen da ake yi na cewa zai koma Manchester City a wannan kakar.

Kyaftin din tawagar ta Ingila, Harry Kane ya ce zai ci gaba da zama a Tottenham a kakar bana, zai mayar da hankali kan samarwa da kungiyar nasarori kamar yadda ya saba yi duk shekara. Tun farko an sa ran Manchester City ce za ta dauki dan kwallon a kakar nan, bayan da ya nemi izinin barin kungiyar daga shugaban kungiyar Daniel Leby, sai dai Leby bai yadda ya kulla wata sabuwar yarjejeniya da dan wasan mai shekara 28 ba.

Kane ya buga wa kungiyar wasan farko a bana a Premier League da Tottenham ta je ta doke Wolberhampton 1-0 a Molineud, kuma kociyan kungiyar, Nuno Espirito Santos ya ce labari ne mai kyau da Kane ya kawo karshen makomarsa a Tottenham da cewar zai ci gaba da zama.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta  Pacos de Ferreira a Europa Conference League ranar Alhamis, bayan da ta yi nasara a wasan farko da ci 1-0 a fafatawar cike gurbi. Kane wanda kwantiragin sa zai kare a karshen kakar wasa ta 2024, ya sanar zai ci gaba da buga wasa a Tottenham, saura kwana shida a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai ranar 31 ga watan Agusta.

Kyaftin din tawagar Ingila bai buga wa Tottenham wasan makon farko da Tottenham ta ci Manchester City 1-0 a gasar Premier League da karawa da Pacos de Ferreira a Europa Conference League.