logo

HAUSA

Ya dace Amurka ta samar sharadi ga hadin gwiwa tsakaninta da Sin wajen dakile sauyin yanayi

2021-09-06 19:59:49 CRI

Ya dace Amurka ta samar sharadi ga hadin gwiwa tsakaninta da Sin wajen dakile sauyin yanayi_fororder_yanayi

Kwanakin baya manzon musamman na shugaban kasar Amurka kan batun sauyin yanayi John Kerry ya kammala ziyarar aiki da ya kawo a kasar Sin, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suna ganin cewa, babu wani sakamako ko kadan da aka samu a ziyarar da ya kawo kasar Sin, amma hakika lamarin ba haka yake ba, manzon musamman Kerry ya koma kasarsa tare da dabarun kyautuata huldar dake tsakanin kasar Sin da Amurka.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, huldar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Amurka ta gamu da babbar matsala, saboda gwamnatin Amurka ta dauki wasu matakai a jere na tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin, a karkashin irin wannan yanayi, Kerry ya kawo ziyara kasar Sin har sau biyu a cikin watanni shida da suka gabata, inda ya yi shawarwari da manzon musamman kan harkokin sauyin yanayi na kasar Sin Xie Zhenhua, kuma ya yi ganawa da wasu manyan jami’an kasar Sin ta kafar bidiyo, lamarin da ya nuna cewa, duk da cewa, huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala, amma ana sa ran aikin dakile sauyin yanayi zai kasance muhimmin fanni yayin da sassan biyu za su gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu.

Abubuwan da suka faru a zahiri, sun sake shaida cewa, Sin da Amurka za su amfana idan sun yi hadin gwiwa, amma idan sun yi yaki da juna, tabbas babu wanda zai ji dadin hakan, yanzu haka ya dace sassan biyu su gudanar da hadin gwiwa a bangarorin dakile sauyin yanayi, da kandagarkin yaduwar annobar cutar COVID-19, da farfadowar tattalin arziki da sauransu bisa tushen moriyar juna.(Jamila)