logo

HAUSA

Duk Da Yanayin Annobar COVID-19 Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Samun Tagomashi A Watanni 7 Na Farkon Bana

2021-09-06 16:47:10 CRI

Duk Da Yanayin Annobar COVID-19 Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Samun Tagomashi A Watanni 7 Na Farkon Bana_fororder_210906-Sharhi-Ahmad-hoto

Hukumomin gwamnatin kasar Sin da abin ya shafa suna ci gaba da daukar kwararan matakan farfado da tattalin arzikin kasar duk kuwa da yanayin da ake ciki na yaki da annobar COVID-19 a daidai lokacin da ake samun yaduwar kwayar cutar nau’in Delta a kasashe da sassan duniya daban daban. Sai dai wani labari mai faranta rai shi ne, yadda bayanai ke kara fitowa a fili cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana kara samun tagomashi. A bisa dukkan alamu dai, za mu iya cewa, kasar Sin ta shigo shekarar 2021 da kafar dama, domin kuwa tun a farkon shekarar nan tattalin arzikin kasar ke kara samun bunkasuwa cikin hanzari. Alal misali, alkaluman da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin MIIT, ya bayyana cewa, manyan kamfanonin intanet na kasar Sin sun samu bunkasar riba cikin sauri a watanni bakwai na farkon bana. Alkaluman na MIIT sun nuna cewa, kudaden shiga da wadannan kamfanonin suka samu ya karu da kashi 26.3 bisa 100 a watanni shidan farko na wannan shekarar wanda ya kai adadin yuan biliyan 886.9 kwatankwacin dala biliyan 137.34. Haka zalika, ribar ta karu da kashi 28 bisa 100 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata zuwa yuan biliyan 84.29, wanda ya karu da kashi 0.6% daga watan Janairu zuwa Yuni. A cikin fannoni daban daban, kudaden shigar da aka samu daga fannin hidimomin sadarwa da suka hada da wakoki ta intanet, da bidiyo, da wasannin, da yada labarai, sun samu saurin bunkasuwa, kamar yadda alkaluman suka nuna. Kudaden shigar wadannan bangarori ya kai yuan biliyan 494.4 a watanni bakwai na farkon bana, wato ya karu da kashi 18.3 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. Koda yake, za mu iya cewa da ma dai faduwa ce ta zo daidai da zama, domin kuwa, a kwanakin baya ma wasu bayanan da masu ruwa da tsaki a fannin kudaden kasar Sin suka fitar sun bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin na rabin shekara ya kafa muhimmin tubalin cimma nasarar cikakken hasashen da aka yi na shekara. Duk da fama da matsalolin annoba, da kalubalolin ci gaban tattalin arziki na cikin gida da aka fuskanta, tattalin arzikin kasar Sin ya cimma nasarar farfadowa sannu a hankali tun farkon shekarar 2021, lamarin da ya kafa wani muhimmin tushe na cimma nasarar hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma na wannan shekarar, matakin da ya baiwa kasar damar zama a sahun gaba a duniya a matsayin kasa mai tsara tattalin arziki. A watanni shidan farko na wannan shekarar, manyan ma’aunan alkaluman tattalin arziki, da suka hada da bunkasuwar tattalin arziki, adadin marasa ayyukan yi, da alkaluman bukatun kayayyaki na (CPI), sun cimma hasashen da aka yi tsammani, a cewar He Lifeng, shugaban hukumar sauye sauye da bunkasa cigaban kasa, wanda ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoto game da aiwatar da manufofin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma na kasa a taron zaunannen kwamitin wakilan jama’a da aka gudanar a kwanakin baya. Ko shakka babu, kyakkyawan tsarin manufofin kasafin kudin kasar Sin na wannan shekarar ya samar da tallafi ga muhimman bangarorin ci gaban kasar, kana ya bayar da gudunmawa wajen farfadowar tattalin arzikin kasar da kuma inganta zaman rayuwar al’ummar kasar. (Ahmad Fagam)