logo

HAUSA

Salgy Baran ita ce zakara a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan: “Ina so in yi abubuwa domin kasarmu”

2021-09-06 12:45:03 cri

Daga watan Fabrairu zuwa Maris na kowace shekara ne, ake yin jarrabawar shiga jami'a a rukuni-rukuni a duk fadin kasar Afghanistan. Baya ga tashin hankalin da ya addabi kasar a wannan shekara, gami da yaduwar annobar COVID-19, sun sa an rufe makarantu da yawa, amma duk da haka, an gudanar da jarrabawar shiga jami’ai da ake kira “Kankor” kamar yadda aka tsara, wadda ta kunshi tambayoyi guda 160, jimilar makin ta kai 360. Salgy Baran ta zama ta farko a jarrabawar shiga jami’a a wannan shekara, inda ta samu maki kusan 353.

Salgy Baran ita ce zakara a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan: “Ina so in yi abubuwa domin kasarmu”_fororder_1

Wani abin burgewa shi ne, wannan shi ne karo na biyu da mace ta ka kasance ta farko a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan a shekaru  biyu da suka wuce a jere, kuma Salgy ta zama mace ta farko ‘yar kabilar Pashtun a tarihin kasar da zama zakara. Pashtuns kabila ce mafi yawan al’umma a Afghanistan, yawan ‘yan kabilar ya kai kusan kashi 40%, kuma yawancin ‘yan kungiyar Taliban ‘yan kabilar Pashtuns ne.

Labarin Salgy da ta kasance ta 1, ya ja hankulan daukacin kasar, kuma manyan kafafen yada labarai daban daban na Afghanistan ciki har da tashar watsa labarai ta Intanet ta Taliban, sun watsa wadannan labarai daya bayan daya. Har ma tsohon shugaban kasar ta Afganistan Hamid Karzari, shugaban babban kwamitin sulhu na kasa Abdullah-Abdullah da sauran manyan kusoshi da mashahuran mutane, su ma sun taya ta murna a shafukan sada zumunta. Salgy ta zabi yin karatu a cibiyar ilmin likitanci ta Jami'ar Kabul, wanda ita ce zabi na farko na zakarun jarrabawar shiga jami’a na kasar Afghanistan a cikin 'yan shekarun nan.

Salgy Baran ita ce zakara a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan: “Ina so in yi abubuwa domin kasarmu”_fororder_2

A shekarun 1990, karkashin mulkin Taliban, matan Afghanistan ba sa iya aiki da ma karatu a firamare, sakandare ko jami'a. A ranar 29 ga watan Agusta, sabon mukaddashin ministan kula da harkokin ilimin jami’a ya bayyana cewa, a cikin tsare-tsaren ilimi na gaba, za a bar mata su je makaranta, domin su yi karatu, amma za a raba dalibai maza da mata

Ban da wannan kuma, a cewar jami’an ma’aikatar kula da ilimin jami’a na Afghanistan, jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu na kasar, nan ba da jimawa ba za su sake budewa, kuma sun yi alkawarin bai wa malamai albashi.

Salgy Baran ita ce zakara a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan: “Ina so in yi abubuwa domin kasarmu”_fororder_3

Game da wannan Salgy ta ce, "Idan shugabanni na yanzu za su iya cika alkawuran da suka dauka, wato su bar mata su je makaranta domin yin karatu da aiki, hakan zai yi kyau sosai." Ta kara da cewa, “Muddin ina da tabbaci, zan dage in kammala karatuna. Idan yanayin da kasarmu ke ciki bai sauya ba, ina fatan zan je kasar waje don na yi karatu. A takaice dai, ina so in koyi ilmi don in taka rawa kan ci gaban kasarmu.”

An haifi Salgy a cikin wani gida mai matsakaicin karfi a lardin Laghman dake tsakiyar Afghanistan. Kamar yawancin sassan Afghanistan, babu ci gaba sosai a fannin samar da hidimar jinya a wurin. Lokacin da Salgy take da shekaru 7, mahaifinta ya mutu sakacin likitoci. Wannan ne ya sa Salgy ta yanke kudurin koyon aikin likita----“Ina so in zama kwararriyar likita.”

Salgy Baran ita ce zakara a jarrabawar shiga jami’a a kasar Afganistan: “Ina so in yi abubuwa domin kasarmu”_fororder_4

Gaba daya su 11 ne a gidansu, maza 3 da mata 8. Ita ce ta 10. Salgy ta iyayenta masu karfafa gwiwa ne, suna ba ta cikakken goyon baya wajen karatu. Sakamakon karancin matsayin ilimi a makarantun gwamnati a Afghanistan, dalibai da yawa kamar Salgy na bukatar kashe kudi da yawa kafin su yi karatu a cibiyoyin horaswa masu zaman kansu. Ta ce, 'yan uwanta ba su taba sanya ta yi watsi da karatu ba saboda dalilin kudi. Suna gaya mata cewa, “Ki mai da hankali kan karatu kawai, mu za mu biya miki kudin karatun.”

Da take magana game da 'yan matan da ba sa son zuwa makaranta, ko kuma wadanda ba sa son mayar da hankali kan harkokinsu na karatu, Salgy ta ce, "Akwai bukatar mu yi kokarin raya kasarmu, kuma mu ne fatan kasar mu. Dole ne mu dogara da kanmu don kasarmu ta tsaya da kafafunta. Babu da wata kasa da ta wuce Afghanistan. Tabbas ba ma son yanayin da kasarmu ke ciki ya ci gaba da tabarbarewa. Ya kamata mu yi aiki tare don kafa sabuwar Afghanistan. "