logo

HAUSA

Shirye-shirye karkashin dangantakar Sin da Afrika na haifar da dimbin alfanu a fadin nahiyar Afrika

2021-09-06 15:38:27 CRI

Yayin wani katafaren taro shekaru 3 da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin Afrika, sun tsara wani shiri dangane da hadin gwiwar Sin da Afrika, inda shugaban kasar Sin ya gabatar da wasu muhimmman shawarwari 8.

Shekaru uku bayan nan, kawancen Sin da Afrika da kuma hadin gwiwarsu, na kara karfi da zurfi, inda ake aiwatar da wannan shiri da aka tsara a zahiri, lamarin da haifar da dimbin alfanu a fadin nahiyar Afrika.

 

Daga cikin alfanun da aka samu daga wannan shiri akwai tashar jiragen ruwa ta Kribi, dake kasar Kamaru. A cewar daraktan tsare-tsare da kula da muhalli na tashar jiragen ruwa ta Kribi, Alan Patrick Mpila Ayissi, jimilar guraben ayyuka 5,000 da kudin shigar da ya rubanya har sau 15 aka samu daga tashar jiragen ruwan, wadda ita ce irinta ta farko da aka samar a Kamaru.

Cikin hadin gwiwa, kasashen Sin da Faransa da Kamaru ke tafiyar da harkokin tashar da aka kafa a watan Maris na 2018 da kamfanin gine-gine na CHEC na kasar Sin ya gina, inda kuma za a kammala mataki na biyu na tashar a 2023. A cewar Mpila Ayissi, “Kamaru na kan wata turban samun ci gaba cikin sauri bisa taimakon kasar Sin”. Kafa tashar, ta sa Kribi zama birnin dake samun ci gaba da kuma karuwar al’umma. A cewar Armand Guehoada, da ya shafe shekaru 8 yana aiki da kamfanin CHEC, “tashar ta zamani ce sosai, kuma za ta amfani zuri’o’i masu zuwa a nan gaba”.

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya fara aiki ne a matsayin mai kula da harkokin da suka shafi ma’aikata, kuma a yanzu, ya zama mai saye da sayar da kayayyakin da ake shiga da fitar da su daga kasar. Kuma ya gamsu matuka da yanayin rayuwarsa. 

A shekarar 2017, cibiyar kula da yanayin kasa da muhallin halittu ta Xinjiang (XIEG), ta kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da shirin raya muhalli na Great Green Wall na Tarayyar Afrika, da nufin inganta muhallin halittu a nahiyar.

Tarayyar Afrika AU ce ta kaddamar da shirin Great Green Wall a shekarar 2007, inda yake da burin samar da zirin bishiyoyi da ya kai sama da kilomita 8,000 a fadin Afrika, daga kasar Senegal zuwa Djibouti a yankin gabashin nahiyar, domin kandagarkin fadadar Hamadar Sahara zuwa yankin kudanci.

Bisa wannan yarjejeniya, Zhou Na, mataimakiyar mai bincike a cibiyar XIEG, da abokan aikinta, sun yi ziyara tsakanin Hamadar Taklamakan dake jihar Xinjiang ta kasar Sin da Hamadar Sahara, domin musayar dabaru da al’ummar Afrika.

Ta ce burinta shi ne, kai dabarun kasar Sin zuwa Sahara da kuma inganta raya muhalli da rayuwar al’ummar Afrika.

A baya bayan nan, ita da abokan aikinta sun dauki dabaru daban-daban bisa yanayin wurare daban-daban. Misali, takaita watsewar rairayi da zaizayar tuddan rairayi a Mauritania da farfado da filayen ciyayi da suka lalace a Habasha da taimakon fasahar karewa da kula da zirin bishiyoyi domin yaki da zaizayar kasa saboda iska mai karfi a Nijeriya.

Mohamed El Houssein Mohamed Legraa, daraktan hukumar kula da shirin Great Green Wall a Mauritania, ya jinjinawa taimakon fasahohi na kasar Sin.

A cewarsa, Sinawa sun yi zarra a yaki da kwararar Hamada. Sun mayar da Hamada zuwa dazuka. Ya ce a Mauritania suna fama da kwararar Hamada da karancin ruwan sama da tasirin sauyin yanayi. Don haka, suke matukar bukatar dabarun Sinawa.

Idan muka dangana zuwa Mozambique kuma, gonar shinkafa ta Wanbao na zaune ne a gundumar Xai-Xai ta lardin Gaza dake kudancin kasar. An kuma kafa gonar ne karkashin jarin asusun raya Sin da Afrika, wadda kuma ta kasance shiri mafi girma irinsa da Sin ta yi a Afrika.

Bisa kasa mai albarkar noma da ta mallaka, da yanayi mai kyau da dimbin albarkatun ruwa dake wurin, da kuma taimakon Sin, gonar ta mamaye filin da fadinsa ya kai kadada 20,000.

Manomi Milagre Abel Massingue, na daya daga cikin mutane sama da 500 da suka shiga aiki a gonar shekaru 5 da suka gabata, inda ya karbi kwangilar noma kadada biyu. Ya ce a baya-bayan nan, yana iya rubanya amfanin gonar da yake samu ta hanyar amfani da fasahohin kasar Sin.

A cewarsa, rayuwarsa ta inganta, domin a yanzu, gidan siminti ya maye gurbin bukkar da yake zama a baya, kuma an sanya kujeru da sauran kayayyakin amfanin gida a ciki. Ya ce noman shinkafa a Wanbao, ya kyautata rayuwarsa” 

Dalilo Latifo, daraktan raya ayyukan gona da yankunan karkara na lardin Gaza, ya ce gwamnatin kasar Sin na taimakawa Maozambique, kuma wannan gona ta habaka daddaden kawancen dake tsakanin kasashen.

Ya kara da cewa, shirin ya yi gagarumin tasiri wajen bunkasa amfanin gona a yankin, haka kuma zai bunkasa raya ayyukan gona a kasar Mozambique baki daya. (Fa’iza Mustapha)