logo

HAUSA

Dr. Imam Wada Bello: Sanya wa al’umma alluran riga-kafin cutar COVID-19 na da muhimmanci

2021-09-07 14:40:21 CRI

Dr. Imam Wada Bello: Sanya wa al’umma alluran riga-kafin cutar COVID-19 na da muhimmanci_fororder_rBABC1-btzqADOGXAAAAAAAAAAA096_690x518

Kwanan nan ne, gwamnatin Najeriya ta amince da fara amfani da alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar. Game da wannan batu, Murtala Zhang ya zanta da Dr. Imam Wada Bello, babban darakta mai kula da lafiyar al’umma da cututtuka ta ma’aikatar lafiya dake jihar Kano a Najeriya.

Dr. Imam Wada Bello ya fara da bayyana yadda jihar Kano take kokarin dakile yaduwar cutar, da fadakar da al’umma kan muhimmancin kandagarkin cutar. Sa’annan a cewarsa, shigo da alluran kasar Sin cikin Najeriya, na da ma’ana sosai, ganin yadda alluran kasar Sin ke da inganci da aminci da kuma tsaro.

Malam Bahaushe kan ce, rigakafi ya fi magani. Don haka Dr. Imam Wada Bello ya yi kira ga al’umma su kiyaye yanayin tsafta, da maida hankali wajen karbar alluran riga-kafin cutar. (Murtala Zhang)