logo

HAUSA

Kasa da kasa na fatan karfafa hadin gwiwa ta fannin cinikayyar hidimomi

2021-09-03 14:53:36 CRI

Kasa da kasa na fatan karfafa hadin gwiwa ta fannin cinikayyar hidimomi_fororder_2021090215501376893

A jiya Alhamis, aka bude bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin(CIFTIS) a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana manyan matakan da kasarsa za ta dauka ta fannin bude kofarta ga ketare, matakan da suka samu yabo daga kasa da kasa. Lubabatu ta hada mana wani rahoto.

Daga ranar 2 zuwa 9 ga wata, ake gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin a birnin Beijing, kuma kasar Ireland ta kasance kasa bakuwa ta musamman da aka gayyata wajen bikin. A jawabin da ya gabatar a gun bikin, firaministan kasar ta Ireland, Micheál Martin ya bayyana fatansa na cewa,“Akwai wasu fannonin da ba su samu saurin farfadowa ba bayan annobar COVID-19, misali yawon shakatawa da sufurin jiragen sama da sauransu. Jama’ar kasashen Ireland da Sin na matukar fatan gaggauta farfado da hadin gwiwar kasashensu a wadannan fannoni, bisa tabbacin tsaro, a yayin da kuma ake neman gano sabbin fannonin hadin gwiwa. A cikin irin wannan hali ne, bikin CIFTIS zai kasance wata kyakkyawar dama.”

Sai kuma a jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya yi nuni da cewa, cinikayyar hidimomi ta kasance wani muhimmin bangare na cinikayyar kasa da kasa, don haka , kasar Sin tana son hada kanta da sassa daban daban, don su more bunkasuwar cinikayyar hidimomi bisa manufar bude kofa da hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna, ta yadda za a sa kaimin farfadowar tattalin arzikin duniya.

Mataimakiyar babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya(WTO) Madam Anabel Gonzalez ta ce, adadin cinikayyar hidimomi dake cikin tsarin cinikayyar kasa da kasa baki daya ya karu daga kashi 9% a shekarar 1970 zuwa sama da 20% a yanzu haka, kuma an yi hasashen ya zuwa shekarar 2040, adadin zai kai kimanin kashi 1/3, wanda ke nufin cewa, manufofin da ke shafar cinikayyar hidimomi za su kara tasiri a nan gaba. Madam Anabel Gonzalez ta kara da cewa, yanzu haka wasu kasashe mambobin WTO na shawarwari dangane da dokokin da abin ya shafa, tana kuma fatan gwamnatin kasashe mambobin kungiyar za su dauki matakai, don inganta dokokin.

A gun taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta kara tallafa wa kasashen da suka amsa shawarar “ziri daya da hanya daya” wajen bunkasa cinikayyar hidimomi. A game da wannan, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce, Zimbabwe na fatan ganin an inganta hadin gwiwar kasarsa da kasar Sin ta fannonin kiwon lafiya. Ya ce,“Muna godiya ga kasar Sin bisa tallafin da ta samar wa Zimbabwe wajen bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma. Zimbabwe na fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin kiwon lafiya, musamman ma rigakafin cututtuka da kirkire-kirkiren fasahohin ayyukan jinya na zamani.” (Lubabatu)