logo

HAUSA

IOM za ta bullo da shirin tallafawa mutanen da suka fuskanci safarar bil Adama a Najeriya

2021-09-03 10:21:31 CRI

IOM za ta bullo da shirin tallafawa mutanen da suka fuskanci safarar bil Adama a Najeriya_fororder_0903-Ahmad1-IOM

Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM, za ta bullo da wani sabon shiri a Najeriya da nufin kare mutanen da suka fuskanci safarar bil Adama da wadanda aka yi fasa kaurinsu ta barauniyar hanya a lokacin da ake kokarin haurewa da su.

Frantz Celestin, babban jami’in shirin IOM a Najeriya, ya ce, shirin wanda za a kaddamar a Abuja, babban birnin kasar a ranar Talata, zai samar da taimako ga mutane marasa galihu da ake yunkurin yin safararsu.

Shirin mai taken, “Hadin gwiwa kan batun bakin hauri da yadda za a cimma nasarar warware matsalar," shirin zai kuma dakile hanyoyin da ake samun yawaitar safarar bil Adama, a cewar Celestin. (Ahmad)