logo

HAUSA

Tilas ne Amurka ta kawar da cikas wajen binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19

2021-09-03 20:41:38 CRI

Tilas ne Amurka ta kawar da cikas wajen binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19_fororder_0903-01

A kwanakin baya, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta gabatar da rahoton binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, inda aka zargi kasar Sin da ta kawo cikas ga binciken da kasa da kasa suke yi kan gano asalin kwayar cutar. Wannan rahoto bai fadi gaskiya ba.

Bisa shawarar da hukumar lafiya ta duniya wato WHO da kasar Sin suka gabatar a cikin rahoton hadin gwiwarsu, ya kamata a gudanar da aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19 a wurare daban daban na duniya a mataki na gaba. A matsayinta na kasar da ta gaza yin nasarar yaki da cutar COVID-19 da yiwuwar zama kasar da cutar ta fara fita a cikinta, ya kamata kasar Amurka ta zama kasar da za a fi bukatar yin bincike kanta a mataki na gaba. Amma Amurka ba ta son shiga binciken, kana ta zargi kasar Sin kan batun. Kasa da kasa ba su ji dadin abin da aikata ba.

A nata bangare, kasar Sin ta nuna goyon baya ga aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, da yin kokarin samar da gudummawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa wajen yaki da cutar. Alal misali, Sin ta riga ta samar wa kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100 alluran rigakafin, ta kuma sayar da alluran fiye da miliyan 800 zuwa kasashe fiye da 60. Amma Amurka ta boye nata alluran rigakafin, da hana fitar da alluran zuwa sauran kasashen waje, wannan ba aikin jin kai ba ne.

Wannan ya shaida cewa, Amurka ba ta dauki nauyi da yin hadin gwiwa kan aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19 da kuma yaki da cutar ba, ita ce kasar da ta fi kawo cikas ga wadannan ayyuka a duniya. (Zainab)