logo

HAUSA

Fasahar 5G za ta kara gwanintar taron wasannin Olympics na yanayin hunturu na Beijing

2021-09-02 11:18:40 CRI

Fasahar 5G za ta kara gwanintar taron wasannin Olympics na yanayin hunturu na Beijing_fororder_olympics-2022

An taba yin amfani da fasahar 5G a karo na farko a taron wasannin Olympics na yanayin hunturu da aka shirya a Pyeongchang dake kasar Koriya ta Kudu a shekarar 2018, to yaya za a kago abin al’ajabi da fasahar a taron wasannin Olympics na yanayin hunturu na Beijing a shekarar 2022 dake tafe?

Mataimakin darektan cibiyar kula da wasannin yanayin hunturu ta babbar hukumar wasannin motsa jikin kasar Sin Hong Ping ya yi tsokaci a yayin dandali mai taken “Fasahar 5G da taron wasannin Olympics na yanayin hunturu” na babban taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2021 da aka shirya jiya Laraba 1 ga wata cewa, “Ga shi nan dandalin yin tsalle ne, muna iya samun hoton bidiyon jikin ‘yan wasa daga kusurwoyi daban daban, ta hanyar yin amfani da fasahar 5G, daga baya muna iya maimaita bidiyon kamar yadda muke so.”

Hong Ping ya kara da cewa, fasahar 5G tana iya samar da goyon baya ga ‘yan wasa wajen kyautata fasahar wasanninsu, a cewarsa: “Mun hada alkaluman da aka samu yayin sa ido kan atisayen wasannin ‘yan wasa da alkaluman da aka samu ta hanyar yin amfani da jirgin sama maras matuki, daga baya mun aika su zuwa na’urorin zamani da fasahar 5G, ta yadda za a yi nazari ko tantance alkaluma ko bayanai a ko da yaushe.”

Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta samar sun nuna cewa, tun bayan fara amfani da fasahar 5G wajen kasuwanci, kawo yanzu, ayyukan da abin ya shafa sun riga sun kai sama da dubu goma, wadanda suke hada manyan sana’o’in tattalin arzikin kasar da yawansu ya kai 22, misali ana amfani da fasahar 5G a fadin cibiyar birnin Beijing, haka kuma ana amfani da fasahar a daukacin dakuna ko filayen wasannin Olympics na yanayin hunturu na Beijing, da hanyoyin dake hade su, ana iya cewa, duk wadannan sun samar da sharuda masu kyau ga amfanin fasahar 5G a taron wasannin Olympics na yanayin hunturu na Beijing dake tafe.

Masanin nazarin kimiyya da fasaha Qiao Xiuquan shi ma ya ba da misali kan yadda ‘yan kallo wadanda ba su samu damar zuwa filin wasa ba zasu iya kallon wasannin a gida ta hanyar amfani da fasahar 5G da ta VR, yana mai cewa, “Muna iya samar da hoton bidiyon wasannin da fasahar 5G kai tsaye ta hanyar kafa kyamarorin zamani a dukkan kusurwoyin filin wasa, ‘yan kallo suna iya kallon wasannin daga gida ko ofis da tabarau iri na VR, suna iya jin dajin kallon gasa tamkar suna filin wasan.”(Jamila)