logo

HAUSA

An bude taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2021 a kasar Sin

2021-09-01 14:48:42 CRI

An bude taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2021 a kasar Sin_fororder_src=http___inews.gtimg.com_newsapp_match_0_12102551109_0&refer=http___inews.gtimg

Jiya 31 ga watan Agusta, an bude taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2021 a nan birnin Beijing bisa jigon “Zurfafa bunkasuwar fasahar 5G da hadin kai don samun moriya tare”.

Shekaru biyu bayan Sin ta fara amfani da fasahar 5G, Sin ta kafa tasoshin 5G dubu 993, wadanda suke shafar dukkanin birane da kashi 95% na dukkan gundumomi da garuruwa, yawan mutanen da suke amfani da fasahar 5G ta wayar salula ya zarce miliyan 392. Fasahar 5G ta yi hadin gwiwa da yanar gizo, da fasahohin manyan bayanai da AI da dai sauran fasahohi, inda aka fitar da sabbin fannoni ciki har da kiwo lafiya ta 5G da masana’antun yanar gizo ta 5G da bidiyo ta 5G da sauransu.

Shugaban hukumar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin Xiao Yaqing ya ba da jawabi a wajen bikin bude taro a jiya cewa, hukumar za ta ci gaba da bude kofarta da kara hadin kai don ingiza bunkasuwar fasahar 5G. Ya ce: 

 “Fasahar 5G a kasar Sin na samun bunkasuwa ne cikin hadin kai da bangarori daban-daban. Sin za ta ci gaba da mu’ammala da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da kamfanoni na sassa daban-daban a duniya don kafa yanayin samun bunkasuwa mai bude kofa da adalci da rashin nuna bambancin ra’ayi. Sin tana matukar maraba da kamfanonin kasa da kasa da su shiga fannin bunkasa 5G a kasar Sin, don su samu bunkasuwa da ba da gundunmarsu wajen samar da kayayyaki da hidimma masu inganci ga al’umma.”

Mataimakin darektan kwamiitn raya kasa da yin kwakwarima na kasar Sin Lin Nianxiu ya nuna cewa, Sin tana da masu sayayya da yawansu ya kai biliyan 1.4, yawan masu amfani da wayar salula na da dimbin yawa, hakan ya sa ta zama kasuwa mafi girma wajen raya 5G. Ya ce, 

“An samu matsaya daya kan fasahar sadarwa saboda fasahar ta zo a mataki na 5, an more fasahar matuka da yin hadin kai sosai. Abin da ya samar da zarafi mai kyau wajen more ci gaba a wannan fanni. Kwamitin na goyon baya kamfanonin kasashe daban-daban da su inganta mu’ammala da hadin kai game da fasahar 5G da sha’anonin dake da nasaba da ita. Ina fatan samar da yanayi mafi kyau don jawo hankalin kamfanoni daban-daban.”

Game da makomar fasahar 5G, babban sakataren kawancen sadarwa na kasa da kasa Zhao Houlin ya nuna ce, rabin jama’ar duniya ba su da yanar gizo balle wayar salula ta fasahar zamani, kasashen duniya na da nauyin dake wuyansa don taimakawa wadannan mutane wajen samun fasahar sadarwa. Ya ce: 

“Yin kirkire-kirkire da raya tattalin arziki ta yanar gizo na bukatar hadin kai na kut da kut na kasa da kasa. Sin tana yin kira ga kasashe da kamfanoni kasa da kasa da su more dabaru don raya fasahar 5G da yanar gizo na duniya tare. Ina fatan kasuwar Sin za ta more dabarunta da gabatar da shiri irin nata don ba da misali da jagoranci a wannan fanni, don hadin kanta da kasa da kasa, ta yadda za su ba da gudunmawarsu wajen raya al’ummar duniya mai ta’ammali da yanar gizo nan gaba.”(Amina Xu)