logo

HAUSA

Riga kafin COVID-19 ne zai bayyana makomar cigaban Afrika

2021-09-01 10:43:46 CRI

Riga kafin COVID-19 ne zai bayyana makomar cigaban Afrika_fororder_210901-Ahmad2-Tattalin arzikin Afirka

Jami’ai da kwararrun masanan Afrika sun aza ayar tambaya game da makomar tattalin arziki da ci gaban nahiyar kasancewar mafi yawan al’ummun kasashen Afrikan har yanzu ba su samu alluran riga-kafin COVID-19 ba.

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD ECA, ta bayyana cewa, wannan tsokaci na zuwa ne a daidai lokacin wallafa sabbin bayanan tattaunawa game da farfadowar Afrika.

A yayin da take jagorantar tattaunawar ta baya bayan nan, babbar sakatariyar hukumar ECA, Vera Songwe, ta ce abin da zai jagoranci makomar ci gaban tattalin arzikin Afrika shi ne riga-kafin COVID-19.

Kawo yanzu, kashi 2.3 bisa 100 na al’ummar Afrika mai yawan mutane biliyan 1.3 ne aka yiwa riga-kafin, yayin da hukumar dakile cutuka masu yaduwa da Afrika CDC ta sha alwashin yi wa kashi 30 bisa 100 na mutanen nahiyar riga-kafin nan da watan Disambar 2021. (Ahmad Fagam)