Gani Ga Wane…..
2021-09-01 16:52:51 CRI
Yanzu haka dai, sojojin Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO, sun kammala ficewa daga cikin kasar Afghanistan, abin da ke bude wani sabon babi a tarihin kasar da yaki ya daidaita. Wannan ya kara tabbatar da cewa, amfani da wata manufar shiga tsakani ta hanyar soja da kakaba dabi’u da tsarin zamantakewa kan wasu kasashe, ba zai taba yin nasara ba. Kayan aro aka ce, ba ya rufe katara. Wannan ne ma ya sa kullum kasar Sin take kira da a bar kasashe su zabi hanyar raya kasa da ta dace da yanayin su, a kuma daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe ko dai da sunan tsarin na demokiradiya ko kare hakkin bil-Adama. Yanzu dai dabara ta rage ga al’ummar kasar Afghanistan, su zabi tsarin raya kasarsu da kansu ba tare da katsalanda daga wasu kasashen ketare ba, domin kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.
Abubuwan da suka faru a tarihin kasar Afghanistan gami da shaidu a zahiri sun nuna cewa, idan har ana fatan samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki, akwai bukatar kasar Afghanistan ta gina tsarin siyasa mai salon bude kofa da zai kunshi dukkan sassa, ta kuma bijiro da matsakaitan manufofin cikin gida da na ketare masu dorewa, ta katse duk wata hulda da kungiyoyin ’yan ta’adda kwata-kwata.
Kasar Sin dai ta bayyana cewa, za ta ci gaba da tattaunawa da dukkan sassa dake kasar Afghanistan da ma ragowar kasashen duniya, za ta kuma samar da goyon baya da taimako gwargwadon karfinta, don ganin an mai da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, da ma yakar dukkan kungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da kungiyar Islama ta gabashin Turkestan (ETIM) a cikin Afghanistan. Masu fashin baki na cewa, abubuwan da suka faru a Afghanistan, na iya zama izni ga duk wata kasa dake neman kakabawa sauran kasashe tsarin da bai dace da su ba. Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah. (Ibrahim Yaya)