Muhimmancin hada kan kabilu daban-daban ga ci gaban kasa
2021-09-01 09:08:00 CRI
A kwanakin baya ne, aka shirya wani babban taro kan harkokin da suka shafi kabilu daban-daban na kasar Sin karo na biyar, taron dake zuwa tun bayan kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin.
A yayin wannan muhimmin taro, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana muhimmin tunani na karfafawa da kyautata harkokin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin take yi da suka shafi kabilu daban-daban kimanin 56 a fadin kasar, inda ya jaddada cewa, inganta tunanin kafa kyakkyawar makomar al’ummar Sinawa ta bai daya, ita ce alkiblar ayyukan JKS dangane da kabilu daban-daban a sabon zamani, a don haka ya kamata a gudanar da dukkan harkoki bisa wannan tunani.
Haka kuma, wannan tunani na da burin jagorancin jama’ar kabilu daban-daban, da su hada kansu da kawo moriyar juna da yin cudanyar juna wajen kafa kyakkyawar makoma ta bai daya.
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin hadin kai da wajibcin mutunta bambance-bambance dake tsakanin kabilu daban-daban, da hada wadannan abubuwa biyu tare, ta yadda kwanciya za ta biya kudin sabulu. Masu fashin baki na cewa, duk kasar da ba ta hada kan al’ummunta daga dukkan fannoni ba, hakika wankin hula zai kai ta dare. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)