logo

HAUSA

Dole ne sojojin Amurka su nemi gafarar Afghanistan

2021-09-01 14:59:43 CRI

Dole ne sojojin Amurka su nemi gafarar Afghanistan_fororder_37857BE74AC67BA66DB3C6F9B823EEDE8ED4E8A8_size186_w800_h450

Duk lokacin da aka kai hari, a kan mai da hankali matuka kan asarar rayuka da jikkatar mutane a sakamakon harin, musamman ma idan akwai mata da kananan yara a ciki, za a yi matukar nuna bacin rai. Wani al’amarin da ya bata ran mutane ya auku a kwanan baya, inda jirgin sama maras matuki ya kai hari kan gidan fararen hula, wurin da sojojin Amurka suke tunanin cewa akwai dan harin kunar bakin wake na kungiyar IS ya boye a ciki, kafar CNN ta ba da labari cewa, mutane 10 sun rasa rayukansu a sakamakon harin, ciki har da kananan yara 6, wani daga cikinsu shekaru 2 da wani abu ne kawai. Wadannan yara da suka ganewa idonsu babban sauyin Afghanistan, yara ne da da ma suka iya rungumar makoma iri daban-daban, amma yanzu sun mutu.

Ban da wannan kuma, a ranar 26 ga wata, an kai harin kunar bakin wake a filin jiragen sama na Kabul, amma an ce lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 200. BBC ta ruwaito maganar wasu da suka ganewa idonsu na cewa, yawancin fararen hular Afghanista sun mutu ne saboda harbe-harbe da sojojin Amurka suka yi a maimakon harin da aka kai ko mayaka na IS. Don me sojojin Amurka masu matukar kwarewa suka aikata irin wannan kuskure?

Ya yiwu yin harbe-harbe kan farare hula akwai alaka da fushi. Sojojin Amurka 13 sun rasa rayukansu a cikin harin da aka kai musu. A shafukan yanar gizo na sada zumunta, wasu masu gidajen shan giya sun saka hotuna na ajiye kwafuna 13 don nuna ta’azziya ga wadannan sojoji 13 da suka mutu, an kuma gabatar da sunayensu bi da bi. Lamarin da ya fi haddasa asarar sojin Amurka a cikin shekaru 10 da suka gabata, amma ‘yan Afghanistan sun fi yin asara ciki har da sojojin Taliban 28. Jin fargaba ko fushi ba za su zama dalilin da sojin Amurka zasu yi harbe-harbe kan fararen hula ba ko kadan. Watakila a idanun sojin Amurka wadannan alkaluma ne kawai na asarar fararen hula, amma iyalansu yanzu na matukar bacin rai.

Amma, abin mamaki shi ne kafofin yada labarai na Amurka wadanda su kan nuna kwarewa wajen yin bincike kan harkokin kasa da kasa cikin gaggawa sun yi shiru a wannan karo, kuma gwamnatin Amurka dake kiran kanta da suna “Kasa mafi kare hakkin Bil Adama” ta yi biris da asarar rayukan fararen hular, sai dai ta yi kuka saboda mutuwar sojojinta kawai. Ke nan a idanun gwamnatin Amurka, babu wajibcin kare rayukan fararen hular Afghanistan, saboda a ganin wadannan ‘yan siyasa, ba kowa yana da hakkin Bil Adama, ta baiwa mutanenta hakki amma sauran mutane ba su da ikon samun hakkinsu a bisa ma’auninta.

Shekaru 20 da suka gabata bayan Amurka ta tada yakin Afghanista, kawancen sojoji karkashin jagorancin Amurka sau da dama ne sun yi harbe-harbe kan fararen hula ko kai hare-hare bisa kuskure, al’amuran da suka haddasa hasarar rayukan fararen hula da dama. Ya kamata gwamnatin Amurka da kawayenta su daidaita matsayinsu kan wadannan abubuwa, su biya diyya ga fararen hular tare da neman gafararsu game da mawuyancin hali da tashe-tashen hankula da suka haddasa a kasar. Idan laifufukan da suka aikata akwai alaka da laifin yaki, to ana fatan kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa zata gudanar da bincike a kansu, don yiwa fararen hular Afghanista adalci yadda ya kamata. (Amina Xu)