logo

HAUSA

Rahoton Da Hukumar Leken Asiri Ta Amurka Ta Bayar Abin Dariya Ne Ga Duniya

2021-08-30 16:38:20 CRI

Rahoton Da Hukumar Leken Asiri Ta Amurka Ta Bayar Abin Dariya Ne Ga Duniya_fororder_微信图片_20210830162516

BY CRI HAUSA

Kwanan baya, hukumar leken asiri ta Amurka wato CIA ta gabatar da rahotonta na neman gano asalin kwayar cutar COVID-19, duk da cewa ba ta yanke shawarar ainihin sakamakon asalin cutar ba, amma ta dora laifin gaza samun sakamako kan kasar Sin. Fadar White House ta Amurka ta kuma fitar da wata sanarwa don yada jita-jitar wai kasar Sin ta hana yin bincike kan batun.

Daktan Sten H Vermund, shugaban kwalejin kiwon lafiyar jama’a na jami’ar Yale ya nuna cewa, hukumar leken asiri ba ta cancanci gudanar da aikin binciken gano asalin cutar ba, gwamnatin Amurka ta yi amfani da hukumar leken asiri da ta gudanar da wannan aiki don cimma burinta na siyasa ne kawai.

Binciken asalin kwayar cutar aikin kimiyya ne dake bukatar kwarewar masanan kimiyya, aiki ne dake da sarkakiya matuka wanda ke bukatar lokaci mai tsawo. Amma, hukumar ta kwashe kwanaki 90 ne kacal ta fitar da rahoton, abin da ya sabawa tsarin kimiyya, ko shakka babu, matakin ya zama iri daya ne da matakan da Amurka ta saba dauka na dora laifi kan wasu.

Hukumar CIA ta yi kaurin suna wajen yin karya da damfara da kuma sata, shin ko za a amince da rahoto maras gaskiya da ta gabatar?

A halin yauzu, cutar tana yawan sauya nau’inta, tana kan ganiyyarta a duniya. Amurka mai son siyasantar da batutuwan kasa da kasa ta zama wani dutse dake kawo cikas ga hadin kan kasa da kasa wajen yakar cutar, ana matukar yin fushi. Dole ne Amurka ta dawo kan hanyar da ta dace a fannin neman gano asalin cutar ta hada kanta da kasashen duniya, kada ta kawo barazana ga sauran sassan duniya a loakcin da take lalata ita kanta. (Amina Xu)