logo

HAUSA

Yadda ake siyasantar da cutar Covid-19 ya fi cutar ban tsoro

2021-08-30 18:24:00 CRI

Yadda ake siyasantar da cutar Covid-19 ya fi cutar ban tsoro_fororder_微信图片_20210830181252

Mai magana da yawun hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya shaidawa taron manema labaran da aka shirya a kwanan baya cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 a cikin gida ya ragu cikin kwanaki 11 a jere a fadin kasar tun bayan da adadin ya fara raguwa a ranar 16 ga wata, kasar ta yi nasarar dakile yaduwar cutar COVID-19 da ta bulla a baya-bayan nan.

A cikin makwanni biyar ke nan kasar Sin ta shawo kan cutar da ta barke a wannan zagaye, har ta zama kasa ta farko a duniya da ta samu nasara a kan yaki da cutar Covid-19 nau’in Delta.

Sai dai kuma, a kasar Amurka wadda ita ma take fama da cutar Covid-19 nau’in Delta, yanayin annobar ya tabarbare. Alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta fitar sun yi nuni da cewa, ya zuwa ranar 29 ga wata, yawan wadanda suka harbu da cutar a kasar ya zarce miliyan 38.7, a yayin da yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar ya zarce dubu 630, sannan kuma a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an samu karin mutane dubu 45 da suka kamu da cutar. Sai kuma a cewar hukumar lafiyar ta kasar, sakamakon cutar Covid-19 nau’in Delta, yawan masu harbuwa da cutar da yanzu haka ke kwance a asibiti ya zarce dubu 100, adadin da ya kai matsayin koli cikin watanni takwas da suka wuce.

Lalle tambayar ita ce, duk da cewa cutar Covid-19 nau’in Delta ce ake fuskanta, amma me ya sa kasar Sin ta kai ga shawo kanta, a yayin da kuma Amurka da ke sahun gaba a duniya wajen harkokin samar da jinya ta sha kaye.

Bayan barkewar cutar a wannan zagaye, kasar Sin ta ci gaba da daukar matakan da ta saba, sai dai ta kara saurin aiwatar da matakan, abin da ya sa ta sha gaban cutar. Kullum gwamnatin kasar tana rike da manufar mai da jama’a a gaban kome, inda kuma take dora matukar muhimmanci a kan lafiyar al’umma, don haka nan da nan ta dauki kwararan matakai na kandagarkin cutar, ciki har da gudanar da gwaje-gwajen cutar tsakanin al’umma don gano wadanda suka harbu da cutar cikin sauri da kuma killace su da ma wadanda suka yi cudanya da su, a wani kokari na katse hanyoyin yaduwar cutar. Ban da haka, kasar Sin ta kuma yi iyakacin kokarinta wajen warkar da masu harbuwa da cutar, matakin da ya sa a barkewar cutar a wannan zagaye, babu wanda ya halaka sakamakon cutar.

Sai kuma a kasar Amurka, gwamnatin kasar ta danganta tabarbarewar yanayin annobar a cikin gida ga munin cutar nau’in Delta, amma ba tare da fahimtar rashin daukar matakai masu inganci ba. Ban da haka, kwatankwacin daukar matakai na shawo kan cutar, ‘yan siyasar Amurka sun fi mai da hankali a kan ta yaya za ta kai ga dora laifin cutar a kan kasar Sin. Sabo da haka, duk da cewa tawagar masanan kasa da kasa na hukumar WHO ta kai ziyarar binciken gano asalin cutar har sau biyu a kasar Sin, tare da fitar da sakamakon binciken da ke cewa, ba zai yiwu ba cutar ta samo asalinta daga dakin binciken kwayoyin halittu, amma tana ta yayata jita-jita kan cewa, wai cutar ta fito ne daga dakin bincike, tare da matsa wa hukumar lafiya ta duniya lamba da ta gudanar da sabon binciken gano asalin cutar a kasar Sin. A ranar 26 ga watan Mayun wannan shekara kuma, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayar da sanarwar cewa, ya umurci sassan leken asari na kasar da su gudanar da binciken gano asalin cutar, tare da bukatarsu su mika masa rahoto cikin kwanaki 90. Ga shi a ranar 27 ga wata, bayan da sassan leken asirin sun shafe tsawon kwanaki 90 suna “bincike”, sun fitar da takaitaccen bayani na rahoton binciken gano asalin cutar da suka gudanar, sai dai babu shaidu da suka samu game da asalin cutar, amma kuma sun sake nuna yatsa ga kasar Sin, tare da zarginta da kawo tsaiko ga binciken.

Wannan wauta ce da Amurka ta kara yi na siyasantar da batun binciken asalin cutar. Wannan abin da ake kira rahoto bai dogara da shaidun kimiyya ba, haka kuma ba shi da aminci. A hakika dai, tun lokacin da Fadar White House ta umarci sassan leken asirin da su jagoranci aikin binciken asalin cutar a watanni uku da suka gabata, ta kuma samar da “sakamako” a cikin gajeren lokaci, sai kasashen duniya suka gano cewa, makasudin Amurka shi ne amfani da batun gano asalin cutar don “dora laifi” kan kasar Sin.

Cutar Covid-19 tana da ban tsoro, amma yadda ake siyasantar da cutar Covid-19 ya fi cutar ban tsoro. A lokacin da ake fuskantar cutar Covid-19, ya kamata ‘yan Adam baki daya su hada kansu tare da taimakawa juna, a maimakon a siyasantar da batun cutar.(Lubabatu)