logo

HAUSA

Wani Kaya Sai Amale

2021-08-30 15:32:25 CRI

Wani Kaya Sai Amale_fororder_0830-1

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da fadi tashin neman hanyoyi masu bullewa wajen mallakar alluran riga-kafin cutar COVID-19 domin yiwa al’ummarsu da nufin samar da garkuwa ga jikin bil adama don gudun kamuwa da wannan shu’umar annobar wacce ta hana duniya sakat. Sai dai wani abin sha’awa shi ne, yadda kasar Sin ta himmatu wajen tallafawa kasa da kasa domin sauke nauyin dake bisa wuyanta, musamman wajen ba da gudunmawar alluran riga-kafin wadanda kamfanonin kasar Sin suka samar bayan da suka samu amincewar hukumar lafiya ta duniya WHO game da ingancinsu. Kididdiga ta nuna cewa, kasar Sin tana kan gaban dukkan sauran kasashe wajen ba da gudummawar alluran riga kafin COVID-19 a duniya. Kamar yadda wani rahoto da masanin cututtuka masu yaduwa a jami’ar Redeemer dake Najeriya Christian Happi, ya bayyana cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Associate Press (AP) ya wallafa a kwanan baya cewa, ya zuwa yanzu, kasar Sin ce ke kan gaban sauran kasashe a duniya, wajen bayar da gudummawar alluran riga kafin COVID-19 a duniya, yayin da gudummawar da sauran kasashe musamman masu karfi ke bayarwa, bai taka kara ya karya ba, bisa la’akari da alkawuran da suka yi. Masanin ya bayyana cewa, gudummawar da irin wadannan kasashe ke bayarwa, ba su wadatar ba, sannan babu tabbas, musamman baya ga yadda suka boye galibin alluran da aka samar a duniya, sannan kuma suna yiwa hatta ma yara riga kafin, har ma suna duba yiwuwar kara bayar da alluran a karo na uku. Rahoton ya kuma lura cewa, baya ga shirinta na fitar da alluran zuwa kasashen ketare, kasar Sin ta kuma sanar da shirin bayar da gudummawar dalar Amurka miliyan 100, don taimakawa wajen kara samar da alluran ga kasashe masu tasowa. Nahiyar Afrika na daga cikin yankunan da suka ci gajiyar gudunmawar riga-kafin COVID-19 daga gwamnatin Sin, inda ta bayar da gudunmawar riga-kafin ga kasashen Afrika da dama. Tun bayan barkewar annobar ta COVID-19 a karshen shekarar 2019, Sin da Afrika suke ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu wajen yaki da cutar, koda a karshen wannan mako, wasu kungiyoyi masu zaman kansu na Sin da Afirka sun yi kira da a kawo karshen nuna wariyar launin fata game da rabon alluran riga kafin COVID-19, shugaban kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama’ar kasar Sin, Lin Songtian, da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu 22 daga kasashe 19 na Afirka, sun rattaba hannu tare kan wata wasika da suka rubutawa Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, inda suka yi kira ga hukumar cewar ci gaba da yaduwar annobar COVID-19 yana matukar barazana ga rayuwar jama’ar Afirka, da kuma haifar da mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, har ma da yin cikas ga saurin farfadowar kasashen Afirka. Dukkan kungiyoyin, sun yi kira da babbar murya da a kawo karshen nuna wariyar launin fata kan rabon alluran riga kafin, da daukar kwararan matakai don tallafawa Afirka, suna masu cewa ta haka ne za a iya taimakawa Afirka wajen tinkarar annobar yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)