Lawal Saleh: Jihar Tibet ta bunkasa sosai sakamakon jagorancin gwamnatin kasar Sin gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar
2021-08-31 14:14:57 CRI
A bana ne ake cika shekaru 70, da cimma nasarar ‘yantar da yankin Tibet na kasar Sin cikin lumana. Kwanan nan ne aka yi shagulgula a birnin Lhasa, fadar mulkin Tibet, inda al’ummun jihar mai cin gashin kai, ke cike da farin ciki da manyan sauye-sauye da suka gani cikin wadannan shekaru 70.
Lawal Saleh, wani mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum, kana masanin harkokin kasashen waje dake birnin Abuja na tarayyar Najeriya. A zantawarsa da Murtala Zhang, Lawal Saleh ya yi takaitaccen bayani kan jihar Tibet ta kasar Sin, da bayyana ra’ayinsa kan dalilin da ya sa jihar ta samu babban ci gaba da manyan sauye-sauye a wadannan shekaru.
A karshe, malam Lawal Saleh ya jaddada cewa, Tibet, yanki ne da ba za’a iya balle shi daga kasar Sin ba, kuma tabbas kasashen duniya sun amince da shi. (Murtala Zhang)