logo

HAUSA

An saki dalibai 92 da aka sace a arewa masu tsakiyar Nijeriya

2021-08-28 16:35:21 CRI

An saki dalibai 92 da aka sace a arewa masu tsakiyar Nijeriya_fororder_微信图片_20210828163436

Gwamnan jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Nijeriya, Abubakar Sani Bello, ya ce an saki mutane 92 da suka hada da dalibai 90, bayan sun kasance a hannun ‘yan bindiga tsawon kimanin watanni 3, bayan harin da suka kai makarantarsu.

Gwamna Abubakar Bello ya bayyana yayin wani taron manema labarai a Minna, babban birnin jihar cewa, ‘yan bindigar da ba a san adadinsu ba, sun kai hari makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko dake garin Tegina na yankin karamar hukumar Rafi ta jihar a ranar 30 ga watan Mayu, inda suka yi awon gaba da dalibai 91 da wasu mutane 2 dake wucewa ta makarantar a lokacin aukuwar harin.

Ya kuma yabawa jami’an tsaro da na gwamnati, wadanda suka taimaka wajen ganin an saki daliban a ranar Alhamis, sai dai bai yi karin bayani kan yadda aka sake su ba, ko an biya kudin fansa ko kuma a’a.

Ya kara da cewa, daya daga cikin yaran ya rasu. Don haka, jimilar mutanen da aka saki ya zama 92. Inda ya ce jami’an lafiya na jihar sun duba lafiyarsu kuma sun tabbatar da cewa za a iya mika su ga iyalansu, sai dai 4 daga cikinsu na bukatar karin kulawar lafiya.

Gwamnan ya kara da bayyana damuwa game da yadda bata gari ke gudanar da munanan ayyukansu, yana mai cewa lamarin ka iya sanyaya gwiwar iyaye wajen tura ‘ya’yansu makaranta.

Ya kuma yi alkawarin gwamnati za ta kama tare da gurfanar da bata garin. (Fa’iza Mustapha)