logo

HAUSA

Kamfanin Huawei za ta taimaki samar da birni mai aminci da fasahohin zamani mafi girma a duniya a kasar Pakistan

2021-08-27 14:37:34 CRI

Kamfanin Huawei za ta taimaki samar da birni mai aminci da fasahohin zamani mafi girma a duniya a kasar Pakistan_fororder_210827-Faeza3

Katafaren kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei da shirin tsara birane na Ravi wato RUDA, na lardin Punjab na gabashin Pakistan, sun ratabba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin samar da birni mai aminci da fasahohin zamani mafi girma a duniya, wanda ke bakin kogi. 

Bisa yarjejeniyar, bangarorin biyu za su hada hannu wajen farfado da kogin Ravi dake kan hanyar lalacewa, ta yadda zai zama birni mai aminci kuma na zamani, da zai dace da raya muhalli ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zamani.

Bangarorin za su hada hannu wajen samar da dazuka na zamani a matakan tsara fasali da gini ta hanyar amfani da fasahohi kamar na IoT da Cloud da manyan bayanai na Big Data da fasahar AI da cibiyar tattara bayanai da rumbunan adana bayanai da tsarin sa ido ta hanyar amfani da na’ura da makamashin hasken rana da sauransu.

Da farko a ranar Laraba, firaministan Pakistan Imran Khan, ya kaddamar da dajin zamani na farko da fadinsa ya kai kadada 1,214 da shirin RUDA zai samar bisa samun taimakon fasahohi daga Huawei.

A cewar Imran Khan, za a dasa bishiyoyi miliyan 10 a dajin, yana mai cewa, za a sa ido kan kowace bishiya da hadin gwiwar Huawei, inda kamfanin zai sanya na’urorin sensor a dajin, wadanda za su rika bada sanarwa idan an yanke wata bishiya. (Fa’iza Mustapha)