Shenzhen: Sauyi daga wata gunduma zuwa wani babban birni
2021-08-27 15:45:15 CMG
Shenzhen wani babban birni ne cikin lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, wanda ke dab da bakin teku da kogin Zhujiang, kuma yana kusa da yankin Hong Kong na kasar Sin. Fadin birnin ya kai muraba’in kilomita 1953, kana yawan mutanen da suke zaune a birnin ya kai miliyan 17.56 a karshen shekarar 2020. Wannan birni yana da wani matsayi na musamman, wato daya daga cikin yankunan musamman na raya tattalin arziki na kasar Sin. Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta ba shi wannan matsayi ne a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 1980, wanda ya sa Shenzhen ya samu damar raya kansa, daga wata karamar gunduma zuwa wani babban birni mai karfin tattalin arziki matuka.