logo

HAUSA

Alkaluman GDP na Nijeriya ya karu a rubu’i na 2

2021-08-27 14:28:42 CRI

Alkaluman GDP na Nijeriya ya karu a rubu’i na 2_fororder_210827-Faeza2 Nigeria GDP

Hukumar kididdiga ta Nijeriya, ta ce alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar, sun karu da kaso 5.01 a rubu’i na 2 na bana.

Cikin rahoton da ta fitar da ya shiga hannun Xinhua a jiya Alhamis, hukumar ta ce alkaluman sun nuna an samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da karuwar kaso 0.51 da aka samu a rubu’in farko, lamarin da ke nuna cewa harkokin kasuwanci da na tattalin arziki, sun kusa kaiwa matakin da suke a baya, wato kafin aiwatar da matakan dakile annobar COVID-19.

A cewar hukumar, farfadowar harkoki da ake ci gaba da gani tun daga karshen 2020, da yadda harkokin cinikayya ke farfadowa sannu a hankali da na tafiye-tafiye a ciki da wajen kasar, sun bada gagarumar gudunmuwa ga karuwar da aka samu, idan aka kwatanta da rubu’i na 2 na 2020 a lokacin da aka fara aiwatar da matakan yaki da COVID-19. (Fa’iza Mustapha)