logo

HAUSA

Xi: Yayata ruhin Saihanba domin cimma burin raya tattalin arzikin kasa

2021-08-26 13:30:57 CRI

Xi: Yayata ruhin Saihanba domin cimma burin raya tattalin arzikin kasa_fororder_saihanba

A kwanakin baya babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a birnin Chengde na lardin Hebei, inda ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da manufofin da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara, a nace kan sabuwar manufar raya kasa, tare kuma da yayata ruhin Saihanba, ta yadda za a cimma burin bunkasar tattalin arzikin kasar yayin da ake kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Shugaba Xi Jinping ya je gandun daji, da wuraren kiyaye kayayyakin tarihi, da kauyuka, da unguwannin gine-ginen gidajen kwana tare da rakiyar sakataren kwamitin tsakiya na JKS na lardin Hebei Wang Dongfeng da shugaban lardin Xu Qin, domin gudanar da aikin bincike tsakanin ranar 23 zuwa ta 24 ga wata.

Da yammacin ranar 23 ga wata, shugaba Xi ya je gandun daji na Saihanba a arewancin lardin Hebei da aka kafa a shekarar 1962. A cikin shekaru kusan 60 da suka gabata, masu aikin gina gandun dajin Saihanba suna shan aikin dasa bishiyoyi a waje mai rairayi karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, har sun samar da abin al’ajabi a wurin, inda aka sauya hamada zuwa filin bishiyoyi.

Shugaba Xi ya hau kan dutsen duniyar wata, mai tsayin mita 1900, ya kalli gandun dajin daga nesa, yayin da yake sauraren bayanan da aka yi masa game da aikin da ake gudanarwa a yankin domin kyautata muhalli, da yanayin da gandun dajin Saihanba ke ciki, daga baya ya yabawa kokarin da ake yi, da sakamakon da aka samu a yankin, inda ya jaddada cewa, fadin filayen bishiyoyin da aka dasa a kasar Sin ya kai sahun gaba a duniya, wannan babban sakamako ne da al’ummun Sinawa suka samu, musamman ma a yankin Saihanba, inda aka dasa bishiyoyi a wuraren da fadinsu ya kai kadada kusan dubu 70, lamarin da ya kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya a tarihin gina wayewar kan hallitu masu rai da marasa rai na duniya, a sanadin haka, masu gina gandun dajin Saihanba sun samu lambar yabo ta “mai tsaron duniya”, lambar da ya kasance lamba mafi daraja wajen kiyaye muhalli ta MDD.

Shugaba Xi ya yi yawo a cikin gandun daji, inda ya bayyana cewa, “Abu mafi muhimmanci shi ne hana aukuwar gobara a gandun daji, dole ne a mayar da tsaron gandun daji a gaban kome.”

Xi ya jaddada cewa, ya dace a daidaita huldar dake tsakanin hana aukuwar hadarin gobara da yawon shakatawa, ya zama wajibi a mai da hankali kan tsaron gandun daji, ban da haka kuma ya kamata a kara karfafa nazarin kimiyya kan aikin kula da gandun daji.

Kana ya yi tsokaci cewa, tarihin gina yankin Saihanba tarihi ne mai burge mutane, wanda ya samar da ruhin Saihanba mai ma’anar “yin aiki tukuru domin raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba”, yana mai cewa, “Bari mu yi kokari domin gina kasarmu da raya tattalin arzikin kasarmu tare kuma da bunkasa wayewar kan hallitu masu rai da masara rai yadda ya kamata.”

A safiyar ranar 24 ga wata, shugaba Xi ya yi rangadin aiki a fadar sarakuna ta Chengde, wadda aka gina a shekarar 1703, inda ya duba muhimman gine-gine a wurin domin kara fahimtarsa kan tarihin fadar da aikin kiyaye kayayyakin tarihi da ake yi a nan. Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai arzikin al’adu da kayayyakin tarihi a duniya, ya dace a kiyaye al’adun gargajiyar kasar Sin tare kuma da yayata al’adun yadda ya kamata.

Da yammacin ranar, Xi ya je kauyen Daguikou na garin Pianqiaozi dake yankin Shuangluan na birnin a cikin mota, domin ci gaba da yin rangadin aiki. Hakika har kullum shugaba Xi yana mai da hankali matuka kan aikin fardado da kauyukan kasar. Da ya shiga dakin kiwon lafiyar kauyen, ya yi nuni da cewa, kamata ya yi a kara karfafa aikin gina kayayyakin more rayuwar jama’a, da aikin samar da hidimomin jama’a a kauyuka, haka kuma ya dace a kara karfafa aikin gina wayewar kai a kauyuka ta hanyar yayata salon rayuwa na kiyaye muhalli.

Daga baya Xi ya je cibiyar kula da tsoffafi dake unguwar Binhe ta birnin Chengde, inda ya nuna cewa, biyan bukatun tsoffafi da samar da tallafi ga tsoffafi domin su kara jin dadin rayuwa, nauyi ne dake bisa wuyan gwamnatin kasar.

Ga kuma tambayar da shugaban ya yiwa masu aikin sa kai, “Kuna jin dadi, ko? E, muna jin dadi sosai, mun zo aikin sa kai a nan ne domin ba da gudummowarmu.”

A filin unguwar, Xi yi hira a mazauna wurin, inda ya bayyana cewa, kabilu 56 na al’ummar Sinawa masu adadin sama da mutane biliyan 1 da miliyan 400 suna zaman jituwa a kasar Sin karkashin jagorancin JKS, tabbas ne za a cimma burin farfado da al’ummun Sinawa.(Jamila)