logo

HAUSA

Sojoji 16 sun mutu sakamakon harin da Boko Haram ta kai a kudu maso gabashin Nijer

2021-08-26 11:30:12 CRI

Ma’aikatar tsaron kasar Nijer ta ba da sanarwa a jiya Laraba cewa, a wannan rana da misali karfe 1 da safe, daruruwan ‘yan Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojoji a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 16 yayin da wasu 9 suka ji rauni. Sojojin sun mai da martani nan take, kuma sun harbe ‘yan bindiga kimanin 50 tare da kwashe dimbin makamansu.

Jihar Diffar tana kan iyakar Nijer da Najeriya, Boko Haram ta rika tada zaune tsaye a wannan wuri a shekarun baya-bayan nan, abin da ya haddasa dimbin asarar rauyuka.

Shekaru fiye da 10 da suka gabata tun kafuwar kungiyar Boko Haram, tana rika kai hare hare kan fararen hula ko sojoji a yankin tabkin Chadi, abin da ya kawo babbar barazana ga kasar Najeriya da Chadi da Nijer da Kamaru da sauransu. A watan Yuli na shekerar 2016, Najeriya da Kamaru da Nijer da Chadi sun yi hadin gwiwa don kafa wata hadaddiyar runduna don yakar Boko Haram. (Amina Xu)