logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane 35 a tsakiyar Najeriya

2021-08-26 09:57:40 CRI

A kalla mutane 35 aka kashe a sabon harin da ’yan bindiga suka kaddamar a daren ranar Talata a jahar Filato dake shiyyar tsakiyar Najeriya, wata majiya daga hukumar ’yan sandan kasar ne ta bayyana hakan.

Majiyar ’yan sandan ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, ’yan bindigar sun hallaka mutane 35 a harin da suka kai kauyen Yelwa Zangam dake yankin karamar hukumar Jos ta arewa a daren Talata, kamar yadda majiyar ta bayyana, an ga mazauna kauyen suna kwashe gawarwakin mutanen da aka kashe a harin domin kai su zuwa majalisar dokokin jahar dake garin Jos, babban birnin jahar.

Simon Lalong, gwamnan jahar Plateau, ya tabbatar cikin wata sanarwa cewa, ’yan bindiga sun afkawa kauyen Yelwa Zangam a daren ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayuka da barnata dukiyoyi.

Lalong ya bayyana harin a matsayin rashin tunani, ya kara da cewa, tuni jami’an tsaro sun kama mutane 10 da ake zargi da hannu wajen kaddamar da harin kuma ana ci gaba da kokarin zakulo dukkan masu hannu wajen shirya harin.

Gwamnan bai bayyan adadin mutanen da harin ya ritsa da su ba, sai dai ya ce ya kafa dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 tun daga karfe 4 na yamma a ranar Laraba a yankin Jos ta arewa domin hana karuwar hare haren. (Ahmad)