Kasashe Dake Dab Da Teku Suna Da Hakkin Neman Diyyar Japan Idan Ta Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya A Cikin Teku
2021-08-26 11:04:12 CRI
Kafar yada labarai ta Japan ta ba da labari a jiya Laraba cewa, gwamnatin Japan da kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo sun yanke shawara cikin hadin gwiwa don zuba ruwan dagwalon nukiliya na tashar makamashi ta Fukushima a cikin teku ta bututun karkashin teku. Idan Japan ta yi biris tare da kin yarda da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi mata ta zuba ruwan dagwalon a cikin teku bisa ra’ayin kashin kanta, to za ta jefa lafiyar daukacin Bil Adama cikin hadari. Kasashen dake makwabtaka da ita a nahiyar Asiya-Pacific da sauran kasashe dake dab da teku suna da hakkin neman diyya daga Japan.
Dole ne Japan ta fahimci cewa, zuba ruwan dagwalon nukiliya ba wani batu ne dake shafar kanta kadai ba, yadda za a magance wannan batu na da alaka matuka da muhallin hallitun teku da lafiyar daukacin Bil Adama.
Bisa yarjejeniyar teku ta MDD, duk wata kasa tana da nauyin dake wuyanta na kiyaye teku. Japan kuma daya daga cikin mambobi dake kulla wannan yarjejeniya da dai sauran yarjejeniyoyi, kada ta manta da nauyin dake wuyanta da hakkinta.
Har ill yau, Japan ba ta dauki mataki ko bayyana matsayinta mai kyau kan wannan batu ba, batun da ya nuna cewa, ita ba wata kasa mai sauke nauyin dake wuyanta ba ne. Idan 'yan siyasar Japan wadanda suke kalubalantar ka'idodin doka na kasa da kasa, da dabi'a, sun dage kan tafiya yadda suke so, za su zama abin ƙima a cikin tarihi. (Amina Xu)