Ci gaban da aka samu a yankin Tibet gagarumar nasara ce ta manufofin bunkasa yankunan kananan kabilu da gwamnatin kasar Sin ta gudana
2021-08-25 09:21:35 CRI
A ranar Talata 19 ga watan Agustan shekarar 2021, ne aka gudanar da wani kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da ’yantar da yankin Tibet cikin ruwan sanyi a birnin Lhasa, babban birnin yankin. Mutane fiye da dubu 20 daga sassa daban daban na yankin Tibet mai cin gashin kansa na kasar Sin ne, suka taru domin murnar wannan rana mai muhimmanci ga yankin.
A shekarar 1951 ne aka sanar da ’yantar da yankin Tibet cikin ruwan sanyi. A cikin shekaru 70 da suka wuce, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta mayar da hankali wajen raya tattalin arzikin Tibet da kuma kyautata zaman rayuwar al’ummar yankin. Bangaori daban daban na kasar Sin sun yi kokari matuka wajen goyon bayan bunkasar Tibet, ta yadda yankin Tibet ya samu gaggarumin ci gaba a tarihi ta fuskar tattalin arziki.
Kafin ’yantar da yankin Tibet cikin lumana, babu hanyar mota a yankin. Amma a yanzu an hada yankin da sassa daban daban na kasar da layukan dogo, da titunan mota da jiragen saman fasinja. Kafin ’yantar da Tibet cikin lumana, adadin wadanda ba sa iya karatu da rubutu a yankin, ya wuce kaso 95 cikin dari. Amma yanzu Tibet ya zama na farko a kasar Sin, wanda ke ba da ilmi kyauta na tsawon shekaru 15.
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban kasar Sin ya bai wa yankin wani allo mai dauke da rubutu domin taya murna, inda ya rubuta kamar haka “ana fatan raya yankin Tibet mai kyau dake cike da farin ciki, a kokarin cimma babban burin farfado da al’ummar Sinawa tare”.shi kuwa Wang Yang, zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin wanda ke shugabantar tawagar wakilan gwamnatin tsakiyar kasar, ya halarci taron, tare da gabatar da jawabi. (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)